An rataye mujahidai a Misra bayan sun saka bam a coci ya kashe kiristoci

An rataye mujahidai a Misra bayan sun saka bam a coci ya kashe kiristoci

- Wata kotu a kasar Masar ta yankewa mutane 17 hukuncin kisa

- Sannan kotun ta kara yankewa wasu mutum 19 daurin rai da rai a gidan kaso

- A watan Nuwambar bara kungiyar IS ta hallaka mutane sama da 300

An rataye mujahidai a Misra bayan sun saka bam a coci ya kashe kiristoci
An rataye mujahidai a Misra bayan sun saka bam a coci ya kashe kiristoci
Asali: Facebook

Wata kotu a kasar Masar ta yankewa wasu mutane 17 hukuncin kisa inda ta kara yankewa wasu mutum 19 hukuncin daurin rai da rai da wasu 10 wadanda zasuyi shekaru 10 zuwa 15 a gidan kaso bisa laifin tada bama bamai.

A shekarar 2016 da 2017 mutane 74 ne suka rasa rayukan su a dalilin hare hare da aka kai musu a kasar ta Masar.

A watan Nuwambar bara kungiyar IS ta hallaka mutane sama da 300 a hare haren da takai.

Tunda kasar ta ture gwamnatin Shugaba Muhammed Morsi a 2013 suka fama da kashe kashen Sojoji da 'yansanda a sanadiyyar jihadin da shuwagannin kungiyar Muslim Brotherhood suka kira a tashi ayi a kasar.

DUBA WANNAN: Kotu: @MBuhari na da damar kwace kadarorin 'barayin PDP'

Shi dai Muhammad Mursi, dama can gwamnatin Mubarak ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai a kurkuku saboda zafin ra'ayin Islama.

Ya haure daga kurkuku ne bayan da masu zanga-zanga suka hambare gwamantin ta Hosni Mubarak da 'ya'yansa a 2011.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel