Gaya mana me kayi da bashin N13Tr da ka ciwo a shekaru ukku - Atiku ga Buhari

Gaya mana me kayi da bashin N13Tr da ka ciwo a shekaru ukku - Atiku ga Buhari

- Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana aiyukan da yayi da Naira tiriliyan 13 da ya ranto a karkashin mulkin shi

- Yace ana ta gunaguni akan Naira tiriliyan 6 da PDP ta ranto a shekara 16 na mulkin ta

- Ya zargi APC da kin maida hankali gurin mulki sai zargi da karya ga Dan takarar PDP

Gaya mana me kayi da bashin N13Tr da ka ciwo a shekaru ukku - Atiku ga Buhari
Gaya mana me kayi da bashin N13Tr da ka ciwo a shekaru ukku - Atiku ga Buhari
Asali: Instagram

Mai neman shugabancin kasa kasa ta karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana yanda ya kashe Naira tiriliyan 13 da ya ranto a cikin shekaru uku na mulkin shi. Yace Naira tiriliyan 6 kacal PDP ta ranto amma ana ta cece ku ce.

A jawabin da tsohon mataimakin shugaban kasar yayi ta bakin kungiyar yakin neman zaben shi a Abuja a ranar laraba, ya zargi APC da rashin aikin yi ta yanda suka bar lamarin shugabancin da sauke hakkokin su, inda suka fi maida hankali da zargi tare da karairayi ga Dan takarar shugabancin kasa na PDP.

"Domin ba wa yan Najeriya ansa, muna so kungiyar yakin neman zaben Buhari da su dauki kalubalen nan ta hanyar ansa wadannan tambayoyi."

DUBA WANNAN: Kididiga ta nuna har yanzu Najeriya ce ta daya a Afirka

"Ku sanar damu aiki daya da Gwamnatin Buhari ta kirkiro, ta fara kuma ta gama a shekaru uku da suka wuce."

"Ku sanar damu matashi daya da yake a Gwamnatin shugaban."

"Ku fadi alkawari daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika."

"ku fada mana suna Dan kudu daya da ke shugabancin cibiyar sirri ta kasa."

"Ku fadi Dan ta'adda daya da aka kama, aka kai shi kotu kuma aka daure shi a karkashin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari," ya rufe.

Atiku ne dai ake sa rai zai baiwa APC babban aikin kayar dashi a badi a zaben shugaban kasa.

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa damu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel