Buhari ya sanya hannu kan dokar hana karkatar da kudi kasashen waje da kaucewa biyan haraji

Buhari ya sanya hannu kan dokar hana karkatar da kudi kasashen waje da kaucewa biyan haraji

- Shugaba Muhammadu Buhari ya saka hannu kan wata muhimmiyar doka

- Sabuwar dokar za ta mayar da hankali ne wajen karbar haraji kan kudade da kadarorin da 'yan Najeriya ke da su a kasashen waje

- A bawa wadanda dokar ta shafa wa'addin watanni 12 domin su cika ka'idojin dokar ko kuma hukuma ta tilasta su

Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka da za ta magance wadanda ke gujewa biyan haraji ta hanyar tserewa da kudadensu kasashen waje mai suna Voluntary Offshore Assets Regularization Scheme (VOARS).

Buhari ya rattaba hannu kan dokar wajabtawa masu kadarori a kasahen waje biyan haraji
Buhari ya rattaba hannu kan dokar wajabtawa masu kadarori a kasahen waje biyan haraji
Asali: Twitter

A sanarwar da ta fito daga bakin hadimin shugaban kasa, Garba Shehu a yau Laraba 10 ga watan Oktoba, ya ce dukkan 'yan Najeriya da ke da kadarori da kudade a kasashen waje za su fara biya musu haraji.

DUBA WANNAN: Anyi kira da Buhari da Tinubu su takawa Oshiomhole birki

Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ne daga ranar Litinin 8 ga watan Oktoban shekarar 2018.

An bawa mutanen da dokar ya shafa watanni 12 domin su cika dukkan ka'idojin dokar kuma su biya harajin da ya dace idan kuma ba haka ba doka ta tilasta musu biya.

Biyan haraji dai nauyi da ya rataya kan dukkan 'yan kasa sai dai abin takaici mutane da yawa basu son biyan harajin har sai tursasa musu biya.

Sanarwar har ila yau ta ce gwamnatin Najeriya za ta yi hadin gwiwa da takwarorinta na kasashen waje domin tabbatar da cewar mutane da kamfanoni sunyi biyaya ga dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel