Hukumar 'yan sanda ta saki dan majalisar wakilai na APC da ta kama jiya

Hukumar 'yan sanda ta saki dan majalisar wakilai na APC da ta kama jiya

Dan mjalisar wakilai, Abubakar Abdullahi Lado, mai wakiltar mazabar Suleja, ya samu 'yancinsa bayan ya shafe guda a kulle a wata boyayyiyar ma'ajiya ta jami'an 'yan sandan SARS dake Abuja.

Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ne ya sanar da hakan yau, Alhamis, yayin zaman majalisar wakilai.

Idab ba ku manta ba, a jiya, Laraba, ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar cikin kasa da sa'o'i 48 da dawowa daga hutun kusan wata uku, majalisar wakilai ta kasa ta yi barazanar rufe zauren majalisar domin nuna fushin su da kama wani mamba na APC, Abubakar Abdullahi Lado, daga jihar Neja da hukumar 'yan sanda ta yi.

Wannan mataki na majalisar ta wakilai na cikin wata takarda da shugaban majalisar, Yakubu Dogara, ya karanta yayin zamanta na yau. Kazalika, majalisar ta kafa kwamitin karkashin shugaban masu rinjaye, Femi Gbajabiamila, da zai sadu da shugaban rundunar 'yan sanda, Ibrahim Idris, kafin majalisar ta dauki wani mataki na shari'a.

'Yan sandan SARS sun kama dan majalisar wakilai na APC daga arewa
majalisar wakilai
Asali: UGC

Toby Okechukwu, wani mamba a majalisar, dan jam'iyyar PDP, daga jihar Enugu, ya bayyana cewar majalisar zata dauki mataki matukar hukumar 'yan sanda ba ta saki Lado cikin sa'o'i 72 ba.

Okechukwu ya bayyana cewar duk kokarin mambobin majalisar na ganin hukumar 'yan sanda ta saki Lado ya ci tura tare da bayyana cewar 'yan sanda sun tsare Lado ne bisa umarnin gwamnan jihar Neja, ba tare da bin doka ko ka'ida ba.

"Abin takaici ne a ce 'yan sanda zasu kama dan majalisa kamar wani dan ta'adda sannan kuma su kafe kan cewar ba zasu sake shi ba sai da izinin gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello. Ina mamakin irin siyasar da muke yi a kasar nan," a cewar Okechukwu.

DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Kotu ta soke dukkan 'yan takara da shugabannin APC a jihar Ribas

Da suke tofa albarkacin bakinsu, wasu mambobin majalisar biyu; Nnenna Ukeje, 'yar jam'iyyar PDP daga jihar Abiya da Nicholas Ossai, dan jam'iyyar PDP daga jihar Delta, sun bayyana bacin ransu da tsare Lado tare da yin korafin cewar yin hakan cin mutunci ne ga majalisar wakilai.

Daga bisani majalisar ta amince tare da bukatar shugaban rundunar 'yan sanda ya tabbatar an sako Lado cikin sa'o'i 24.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel