SGF Boss Mustapha ya tattara ayyukan Gwamnatin APC a littafi guda a wajen taron FEC

SGF Boss Mustapha ya tattara ayyukan Gwamnatin APC a littafi guda a wajen taron FEC

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wani makeken littafi wanda ke dauke da jerin duk ayyukan da Gwamnatin sa tayi daga lokacin da ya hau mulki zuwa yanzu.

SGF Boss Mustapha ya tattara ayyukan Gwamnatin APC a littafi guda a wajen taron FEC
An ba Shugaba Buhari kundin jerin ayyukan da yayi a shekaru 3
Asali: Twitter

Sakataren Gwamnatin Tarayya watau Boss Mustapha ne ya ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan babban littafi wanda aka tattara ayyukan sa daga 2015 zuwa 2017 a taron Majalisar zartarwa watau FEC da aka yi a yau Laraba.

Littafin mai dauke da shafuka 1042 ya shiga hannun Shugaban kasar inda a ciki aka jero irin tsare-tsaren da Gwamnatin na sa ta dabbaka a Najeriya. Mista Boss yace littafin zai zama matattarar shaida cewa Buhari ya cika alkawurun sa.

KU KARANTA: Za a ga cigaba a fannin tattali a Gwamnatin Buhari inji Masana

Boss Mustapha ne ya tattara wadannan ayyuka a wuri guda inda ya gabatarwa Ministoci da sauran manyan Gwamnatin Tarayya irin kokarin da su kayi a mulki. Za dai a raba wannan kundi a sauran Ma’aikatu domin kowa ya shaida.

Tun ba yau ba dama aka umarci Ministocin Shugaba Buhari da su tattara ayyukan da su kayi a wuri guda su ba Sakataren Gwamnatin Najeriya. Yanzu dai ofishin Sakataren ta kammala aikin dunkule wannan ayyuka duk a wuri guda.

Dazu kun ji cewa Alhassan Doguwa wanda yana cikin manyan kuma Jigo APC daga Arewacin Najeriya a Majalisa yayi magana game da batun tsige Yakubu Dogara inda yace babu wannan shiri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel