Biyu babu: Ba mu san da takarar Tambuwal ta gwamna ba - PDP

Biyu babu: Ba mu san da takarar Tambuwal ta gwamna ba - PDP

A yau, Talata, ne shugaban jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Milgoma, ya bayyana basu da dan takarar gwamna jam'iyyar da ya wuce Alhaji Mannir Dan-Iya tare da karyata jita-jitar cewar an maye sunan dan takarar da na gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal.

Da yake magana da manema labarai a Sokoto, Milgoma ya bayyana cewar rahotanni dake yawo a gari cewar an maye suna Dan-Iya da na Tambuwal ba gaskiya bane, basu da tushe balle makama.

Milgoma ya bayyana cewar har yanzu Dan-Iya ne dan takarar PDP ma gwamnan jihar Sokoto. Sai dai ya ce akwai ragowar lokaci, a hukumance, na canja sunan dan takara.

Biyu babu: Ba mu san da takarar Tambuwal ta gwamna ba - PDP
Tambuwal
Asali: Depositphotos

Sannan ya kara da cewar jam'iyyar zata sanar da jama'a idan an samu wani canji tare da bayyana cewar akwai dokoki da ka'idoji da ake bi kafin canja sunan dan takara.

DUBA WANNAN: Buhari ya rubuta wasika zuwa ga Saraki, ya bayyana dalilin kin saka hannu a sabbin dokoki 15

Milgoma ya ce taron da aka yi na ranar 7 ga watan Oktoba a hedkwatar PDP a jihar Sokoto, na nuna godiya ne bisa irin kokarin da Tambuwal ya yi a zaben fitar da dan takara na jam'iyyar da aka yi a garin Fatakwal.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar an shiga yada jita-jitar cewar an gudanar da sabon zaben fitar da dan takarar gwamna a PDP a Sokoto, kuma Tambuwal ne ya yi nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel