Turnuku: Dakarun Sojin Najeriya sun yi gaba da gaba da mayakan Boko Haram a Borno

Turnuku: Dakarun Sojin Najeriya sun yi gaba da gaba da mayakan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar Sojin Najeriya sun yi gaba da gaba da yayan kungiyar ta’addanci ta Boki Haram a yayin da suke sintiri tare da Sojojin sa kai watau civilian JTF a garin Mairari na jahar Borno a ranar Lahadi 7 ga watan Oktoba.

Legit.ng ta ruwaito Sojoji sun samu nasarar kashe guda daga cikin yan ta’addan, sa’annan sauran mayakan na Boko Haram suka ranta ana kare tare da raunukan alburusai da suka sha daga bindigun Sojoji.

KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba yayin da gwamnatin Buhari ta sanar da karancin albashin da za ta iya biyan ma’aikata

Daga cikin makaman da dakarun Sojojin Najeriya suka kwato daga mayakan na Boko Haram akwai bindiga kirar AK 47 guda daya, alburusai da dama, da nakiya. Sai dai yan ta’addan sun raunata guda daga cikin Sojojin sa kai na civilian JTF, wanda a yanzu haka yana samu kulawa.

Daga karshe rundunar Sojan kasa ta bakin Kaakakinta, Birgediya Texas Chukwu ta nemi jama’a da su tabbata sun bata muhimman bayanai game da duk wani abinda suka sani da ya shafi ayyukan Boko Haram don bata damar gamawa da su.

A wani labarin kuma wasu Sojoji guda uku sun kashe wani karamin yaro tare da caka ma mahaifinsa wuka a lokacin da mahaifin yayi kokarin kare matarsa daga wulakancin Sojojin a lokacin da suke cacar baki da ita a kusa da barikin Yansanda dake Wulari na jahar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa da fari dai jama’an dake wurin ne suka fara shiga tsakanin Sojojin da wata budurwa a lokacin da suke dukanta a cikin Keke Napep, sai dai ashe hakan ya bata ma Sojojin rai, inda suka dawo dauke da bindigu sanye da kayan Sojoji.

Daga nan ne mahaifiyar yaron ta shiga cikin jerin jama’an dake gargadin Sojojin akan harbe harben da suke yi a sama, wannan ne ya sanya Sojojin suka fara cacar baki da ita, har ta kai ga fada ya kaure tsakaninsu da mijinta wanda jami’in Dansanda ne, inda suka caka masa wuka tare da bindige yaronsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel