Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar

Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar

Gwamnan jahar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya taya Alhaji Atiku Abuakar murna, wanda ya lashe zaben fidda gwani a cikin jam’iyyar PDP da tsaya mata takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2019.

Legit.ng ta ruwaito Tambuwal ya sanar da taya Atiku murnar ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba dake dauke da sa hannunsa inda ya yi alkawarin taimaka ma Atiku da duk gudunmuwar da yake bukata don cimma burinsa.

KU KARANTA: Idan da ni barawo ne da tuni Buhari ya garkame ni a kurkuku - Atiku

Idan za’a tuna, yan takara masu muradin darewa mukamin shugaban kasar Najeriya ne suka fafata a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da uwar jam’iyyar ta gudanar a garin Fatakwal na jahar Ribas a ranar Asabar 7 ga watan Oktoba.

Takarar shugaban kasa: Gwamna Tambuwal ya yi mubaya’a ga Atiku Abubakar
Atiku da Tambuwal
Asali: Twitter

Sai dai bayan kammala zaben ne sai kallo ya koma sama, inda dan takarar da ake zaton nada goyon bayan jigon jam’iyyar PDP kuma gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike, wato Aminu Waziri Tambuwl ya sha kayi bayan ya samu kuri’u 693, yayin da Atiku mai karfin arziki ya lashe zaben da kuri’u 1, 532.

“A madadina da iyalaina da miliyoyin magoya bayana daga dukkanin sassa da bangarorin kasarnan, ina tayaka muka murnma da zuciya daya, tare da tayaka farin cikin wannan nasara da ka samu na samun tikicin takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.

“Nasarar da ka samu a zaben gaskiya da adalci ya nuna jam’iyyarmu ta PDP ta yi gyara, kuma hakan ya zamto sako mai karfi da jam’iyyar take isarwa ga yan Najeriya game da manufarta na ganin ta karkatar da akalar kasarnan ta hanyar samar da cigaba mai daurewa.” Inji shi.

Daga karshe Tambuwal yayi alkawarin hada hannu da Atiku don ganin ya samu nasara a zaben shekarar 2019, sa’annan yayi kira ga yayan jam’iyyar PDP dasu nade hannayen rigunansu domin kuwa yanzu za’a fara aiki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa za ta koma LEGIT.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel