Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP

Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP

Dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya yi jawabi bayan ya yi nasara a zaben fidda gwani da aka gudanar a Port Harcourt a ranar Lahadi 7 ga watan Oktoban 2018.

Atiku ya lashe zaben ne bayan ya fafata da 'yan takara 11 da ke neman tikitin takarar shugabancin kasa na jam'iyyar inda ya samu kuri'u 1,532 yayin da mai biye masa Gwamna Aminu Tambuwal ya samu kuri'u 693.

Ga wasu muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a cikin jawabin da ya yi bayan nasarar lashe zaben fidda gwanin.

1. Biyaya da jam'iyya da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar

Atiku ya jadada biyayarsa ga jam'iyya da masu ruwa da tsaki musamman Ciyaman din jam'iyyar na kasa, Uche Secondus inda ya ce ba za'a taba samunsa da aikata wani abu da ka iya kawi cikas ga jam'iyyar ba.

Ya kara da cewa shi da shugabanin PDP ba za su bawa al'ummar Najeriya kunya ba.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 5 da suka fi sauran takwarorinsu a Najeriya

2. Ya yabi tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo

Atiku ya mika godiyarsa ga tsohon mai gidansa bisa zabensa da ya yi a matsayin abokin takara da kuma koyar da shi dabarun shugabanci yayin da suka jagoranci Najeriya tare.

"Ba zan kasance a nan ba idan ba domin damar da tsohon mai gida na, shugaba Olusegun Obasanjo ya bani ba da ya zabe ni a matsayin mataimakinsa.

"Na koyi darrusa sosai daga wajensa kuma nayi imanin abubuwan da na koya daga gareshi za su taimaka min wajen yadda zan jagoranci Najeriya. Hakan yasa na ke mika godiya ta gareshi," inji Atiku.

3. Godiya ga Gwamna Nyesom Wike da Gwamnatin Jihar Rivers

Ya mika godiyarsa da Gwamna Nyesom Wike, gwamnatin jihar Rivers da al'ummar jihar baki daya saboda daukan nauyin taron na jam'iyyar.

"Muna fatan za mu cigaba da aiki tare da gwamna jihar Rivers da al'ummar jihar domin ganin jam'iyyar mu ta kwace mulki a zaben shekarar 2019," inji Atiku.

4. Ya yabi sauran 'yan takarar shugabancin kasa na PDP

Tsohon shugaban kasar ya yabawa sauran 'yan takarar jam'iyyar PDP saboda yadda suka nuna dattaku da bashi goyon baya bayan ya yi nasarar lashe zaben.

Atiku ya ce a shirye ya ke ya yi aike tare da dukkansu domin ganin jam'iyyar ta kai ga nasara.

"A shirye na ke inyi aiki tare da dukkanku domin samun nasara a 2019 domin ba zan iya dukkan aiki ni kadai ba," inji shi.

5. Ya yabawa wadda suka tsara taron kasar na PDP

Atiku Abubakar ya ce zaben na PDP shine zabe mafi inganci da tsafta da aka gudanar tun dawowar Najeriya kan tafarkin Demokradiyya a shekarar 1999. Ya ce tarihi ba za ta manta da wannan taron ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel