2019: Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri

2019: Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri

Mun samu labari cewa daya daga cikin masu takaran Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Rabiu Musa Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri a bainar jama’a a jiya.

2019: Kwankwaso ya ba tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan hakuri
'Dan takaran PDP ya nemi afuwar tsohon Shugaban kasa
Asali: Depositphotos

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ba Dr. Goodluck Jonathan hakurin abin da ya faru a baya lokacin yana mulki. Rabiu Kwankwaso ya nemi Jonathan da Mataimakin sa watau Namadi Sambo su yafe masa sa-in-sar su a baya.

‘Dan takarar Shugaban kasar yayi wannan jawabi ne jiya da dare lokacin da aka ba masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP minti 5 su yi takaitaccen jawabin inda su ka dosa kafin a fara zaben fitar da gwani a jiya.

KU KARANTA: 2019: Babu fastocin Bukola Saraki wajen babban taron PDP

Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya nuna cewa a lokacin da, sun dauka cewa ba a taba samun shugabancin da ya tabarbare irin sa’ar da Jonathan yake mulki ba. Kwankwaso yace sai dai yanzu an yi walkiya sun gane gaskiyar zance.

Yanzu dai ana neman tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa a PDP Tanimu Turaki, Sule Lamido, Attahiru Bafarawa. Sauran ‘Yan takarar sun hada da Dr. Yusuf Baba-Ahmed, Ahmad Makarfi, da Ibrahim Dankwambo da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel