An kara kashe wani sojan Najeriya a jihar Filato

An kara kashe wani sojan Najeriya a jihar Filato

A kalla mutane 4, cikinsu har da jami'in sojin Najeriya, aka tabbatar da kisansu a wani harin tsakar daren Alhamis da aka kai a kauyen Nkiendoro a karamar hukumar Bassa dake jihar Filato.

Jaridar Premius Times ta rawaito cewar ko a ranar Talata sai da aka kashe wasu mutane 13 a wani harin da aka kai kauyen Jol dake karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Manjo Adam Umar, kakakin rundunar soji ta "Operation Safe Haven" a jihar Filato, ya tabbatar da kai harin na ranar Talata tare da bayyana cewar tuni sun aika jami'an soji yankin domin tabbatar da zaman lafiya

"An kashe farar hula 3 da jami'in tsaro 1. An raunata wani jami'in tsaro guda," a cewar manjo Umar.

"Harin na Jol na zuwa ne a matsayin na daukan fansa bayan kisan wasu shanu 3 na Fulani da aka yi ranar 19 ga watan Satumba. Duk da an yi masu sulhu, sai aka kara kashe wani makiyayi da shanunsa 5 tare da raunata wasu a ranar 29 ga watan Satumba.

An kara kashe wani sojan Najeriya a jihar Filato
Sojojin Najeriya
Asali: Facebook

"Bayan wannan hare-haren, an kara kashe wani yaron makiyaya ta hanyar harbinsa a ka da kashe masa saniya a ranar biyu ga watan Oktoba, ranar da aka kai wani hari a wani kauyen kabilar Berom a Jol da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 tare da kone gidaje," kamar yadda manjo Umar ya fada.

Premium Times ta kara rawaito cewar an kashe mutane 19 a wani hari da aka kai kauyen Ariri na karamar hukumar Bassa.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Bayan gano motar sa, sojoji sun kama wani mutum sanye da kakin janar Alkali, hoto

Hukumomin 'yan sanda da na soji basu tabbatar da wannan labari ba har zuwa lokacin da jaridar ta wallafa rahoton.

Sai dai Sunday Abdul, shugaban kungiyar cigaban Irigwe (IDA) ya tabbatarwa da jaridar Premium Times batun kai harin na ranar Laraba

"An kai harin ne a daren jiya (Alhamis) lokacin da jama'a su ke bacci. An kashe mutane 19, kuma mun sanar da hukumomin tsaro. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato ya ziyarci kauyen da aka kai harin da safiya yau (Juma'a)," a cewar Mista Abdul.

Duk da kiraye-kirayen da shugaba Buhari, gwamna Lalong na jihar Filato da malaman addini suka yi a kan jama'a su zauna lafiya, har yanzu ana cigaba da kai hare-hare a jihar Filato.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel