Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC

Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC

- Wata babbar kotu ta yanke hukuncin kisa ga direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC

- Direban ya kashe jami'in ne a shekarar da ta gabata, ta hanyar kade shi da mota a jihar Kebbi

- Hukumar FRSC ta ce akalla jami'ai 74 ne suka gamu da ajalinsu a hannun direbobi masu tukin ganganci

Wata babbar kotun jiha da ke da zama a Birnin Kebbi ta yanke hukuncin kisa ga Usman Aliyu, wanda aka fi sani da Kwastoma, direban da ya shahara wajen ganganci da mota, wanda ya kashe RMA (III) Muhammad Babangida, a shekarar da ta gabata.

Kisan ya faru ne a lokacin da Babangida, jami'in hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, da ke aiki a jihar Kebbi, ya ke kan bakin aiki.

A cewae wata sanarwa da aka bayar a jiya Juma'a daga hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, Bisi Kezeem, ta bayyana cewa lamarin ya auku a kan hanyar Ahmadu Bello a babban birnin jihar, Birnin Kebbi a ranar 3 ga watan Afrelu, 2017.

Sanarwar ta bayyana rahotannin da ta tattara sunyi nuni da cewa Usman Aliyu direba, na tuka mota baka korar Toyota Corolla saloon, mai lamba, KLG 342 AA a ranar da ya yi kokari bi takan wani jami'in hukuar Abubakar Garba Abubakar.

Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC
Kotu ta yanke hukuncin kisa akan direban da ya kashe wani jami'in hukumar FRSC
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Al'ajabi: Wakilan APC 6 sun mutu jim kadan bayan jefa kuri'arsu a Jigawa

"Sai dai bai samu nasarar buge jami'in ba, wannan ne ya sanya shi kai farmaki ga abokin aikin Abubakar, wato Muhammad wanda ke tsaye yana aiki a kan titin, inda kuma ya yi nasarar hawa ta kanshi, wanda ya mutu nan take.

"Wanda ake zargin da kotu ta yankewa hukuncin kisa a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, 2018, a ranar da ya aikata kisan kan, ya tsere, sai dai rundunar yan sanda sun samu nasarae cafke shi a kan hanyar Kalgo bayan da muka sanar da su," a cewar sanarwar.

Idan ba a manta ba Legit.ng ta ruwaito maku cewa shugaban hukumar FRSC, Dr Boboye Oyeyemi, ya bayyana cewa akalla jami'an hukumar 74 ne suka gamu da ajalinsu a hannun direbobi masu tukin ganganci, yana mai gargadar direbobi akan hawa kan jami'ansu.

Sanarwa: Nan bada dadewa ba, shafin Hausa.legit.ng zai sauya suna zuwa Hausa.legit.ng. Hakika wannan babban ci gaba ne kuma muna fatan zaku cigaba da kasancewa tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel