Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara

Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara

Dan majalisar wakilai na jihar Yobe, Hon Abdu Mamman Zoto ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) zuwa jam'iyyar adawa ta People’s Democratic Party (PDP) domin ya samu tikitin takara.

Dan majalisar mai wakiltan yankin Damagun ya shaidawa manema labarai yau a Damaturu cewar ya fice daga APC ne saboda matsin lambar da wasu masu adawa da shi suke masa.

Ya ce an mayar da mazabarsa saniyar ware wajen ayyukan more rayuwa da wasu tsare-tsaren gwamnati da zai kawo cigaba ga jama'ar yankinsa.

Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara
Dan majalisar APC ya koma PDP bayan rasa tikitin takara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron sulhu, sun kashe jagoran Fulani tare da raunana 'yan sanda 2

"Ina fuskantar matsin lamba daga jam'iyya duk lokacin da nayi kokarin kawo tsare-tsaren da za su kawo alkhairi ga mutanen yanki na."

"Tunda jam'iyyar ba za ta bani damar kawo canje-canjen da za su kawo alkhairi ga mutanen mazaba ta ba, sai na yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP da zata bani goyon bayan da na ke bukata."

"Abinda ya fi muni cikin muni shine yadda jam'iyyar APc ta cire dukkan magoya baya na daga cikin jerin sunayen deliget kuma suka doge cewar sai anyi zaben fidda gwani a inda bani da mogaya baya ko daya".

"Na tuntubi jami'an PDP a jihar Yobe, suka karbe ni hannu biyu-biyu saboda sun san ina da magoya baya a mazaba ta. PDP ta bani tikitin takara ba tare da hamayya ba a zaben 2019." inji Zoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel