'Yan bindiga sun tarwatsa taron sulhu, sun kashe jagoran Fulani tare da raunana 'yan sanda 2

'Yan bindiga sun tarwatsa taron sulhu, sun kashe jagoran Fulani tare da raunana 'yan sanda 2

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari a karamar hukumar Demsa da ke jihar Adamawa a ranar Talata yayin da ake gudanar da taron sulhu da makiyaya inda suka kashe mutum guda daya.

Mai magana da yawun Fulani, Usman Ali, ya shaidawa manema labarai jiya a Yola cewar an kaiwa wasu Fulani hari yayin da suke wata zaman sulhu da Basaraken Bata, Hama Bata, Ahmadu Teneke ya shirya.

Ali ya ce a kwanakin baya wasu 'yan bindigan sun kashewa Fulani shanu 20 ba tare da watta hujja ba hakan yasa 'yan kungiyar suka kai kara ofishin 'yan sanda da ke garin Demsa.

'Yan bindiga sun tarwatsa taron sulhu, sun kashe jagoran Fulani tare da raunana 'yan sanda 2
'Yan bindiga sun tarwatsa taron sulhu, sun kashe jagoran Fulani tare da raunana 'yan sanda 2
Asali: Depositphotos

Ya kuma ce Fulanin sun kai kara wajen Basaraken masarautar Bata saboda ya dauki mataki a kai, hakan yasa basaraken ya umurci hakimin yankin ya zauna da bangarori biyun domin a sulhunta tsakaninsu.

DUBA WANNAN: Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara

"Shanun suna kiwo a daji ne kawai wasu mazauna kauyen suka kai musu hari. Shanun basu shiga gonar kowa ba kuma babu wata rashin jituwa da ta faru tsakanin mazauna kauyen da makiyayan," inji Ali.

Ali ya yi kira ga gwamnatin jihar da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro sun binciko wadanda suka kai wannan harin tare da hukuntasu kamar yadda doka ta tanada.

Kakakin 'yan sandan jihar, Othman Abubakar ya tabbatar da afkuwar harin inda ya ce wasu Fulani sun kai karar cewa an kashe shanunsu a Kademun kuma da 'yan sanda suka tafi wajen domin ganin abinda ke faruwa sai aka far musu.

"Har yanzu akwai wani bafulatani daya da ba'a gano inda ya ke ba kuma 'yan sanda sun kwato babura guda 4 mallakar makiyaya," inji Abubakar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel