Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani

- Babban kotun da ke Kaduna ta dakatar da jam'iyyar APC da INEC daga gudanar da zabe a jihar Kaduna

- Kotun ta bayar da wannan umurnin ne bayan jam'iyyar ta bawa Shehu Sani tikitin takarar kujerar Sanata ba tare da an gudanar da zaben fidda gwani ba

- Matakin da jam'iyyar ta dauka ya sanya daya daga cikin masu neman tikitin takarar Sanata a jihar, Uba Sani ya shigar da kara domin a bi masa hakkin sa

A jiya, Laraba ne Babban Kotun da ke Kaduna ta dakatar da jam'iyyar APC daga gudanar da zaben fidda gwani na zabar dan takarar Sanata a yankin Kaduna ta Tsakiya.

Wannan umurnin kotun yana zuwa ne bayan magoya bayan Uba Sani sunyi zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar a daren Talata inda suke bukatar jam'iyyar ta sauya matakin da ta dauka na bawa Shehu Sani tikitin zabe kai tsaye da bare da zabe ba.

Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani
Tana kasa tana dabo: Kotu ta takawa APC burki a kan zaben Shehu Sani
Asali: Depositphotos

A bangerensu, wata kungiya mai goyon bayan Shehu Sani ta bukaci uwar jam'iyyar tayi watsi da wannan kirar na magoya bayan Uba Sani da gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

DUBA WANNAN: Matsin lamba daga EFCC: Tsohon gwamnan PDP Shema ya garzaya kotun daukaka kara

Sa dai tuni Mallam Uba Sani mai neman takarar Sanata na yankin Kaduna ta Arewa ya garzaya kotu inda ya yi karar uwar jam'iyyar kan matakin da ta dauka na bawa Uban Sani tikitin takarar jam'iyyar.

Uba Sani dai shine dan takarar da gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya zabe domin darewa kan kujerar mulkin Sanata na yankin na Kaduna ta Tsakiya.

A halin yanzu, babban kotun ta umurci Ciyaman din APC na kasa Adams Oshiomhole da INEC da Shehu Sani su koma kan tsarin da ake a baya har zuwa rabar 2 ga watan Oktoba da za'a yanke hukunci saboda hana Uba Sani da sauran 'yan takarar fafatawa.

Lauyan Uba Sani, Sule Shuiabu, ya ce Uba Sani ya dauki matakin shigar da jam'iyyar kara a kotu ne bayan ya yi kokarin warware matsalar a jam'iyyance amma hakan ya ci tura.

Kotun ta daga cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel