Siyasar Yanki: Hanyoyi 10 da Rabi'u Kwankwaso zai iya koyar siyasa daga Malaminta Jagaba Bola Tinubu

Siyasar Yanki: Hanyoyi 10 da Rabi'u Kwankwaso zai iya koyar siyasa daga Malaminta Jagaba Bola Tinubu

- Kwankwaso naso ya mamaye siyasar Arewa maso yamma

- Tinubu ya riga ya mamaye kudu maso yamma

- Cikin su biyu waye yaci sunan jagaba?

Tsakanin Kwankwaso da Tinumbu, waye jagaban siyasa na ainahi?
Tsakanin Kwankwaso da Tinumbu, waye jagaban siyasa na ainahi?
Asali: Depositphotos

A yadda siyasa a yanzu ta kacame tsakanin APC da PDP, duba da Tinumbu, yadda yake dauki dora a yankinsa, da yadda shima Kwankwaso ya sami 'yan siyasa na cikin gida yake irin nasa salon, zamu kwatanta muku yadda Tinubu ya buge Kwankwaso yayi masa fintinkau.

Tsakanin Kwankwaso da Tinumbu, waye jagaban siyasa na ainahi?
Tsakanin Kwankwaso da Tinumbu, waye jagaban siyasa na ainahi?
Asali: UGC

A lokutan 1999 dai tare aka zabi Bola Tinubu da Kwankwaso gwamna, kuma dukkansu sunyi siyasa sosai a lokacin mulkin soja, sai dai Kwankwaso ya kasa kawo kujerarsa ta tazarce, yayin da shi kuwa Tinubu ya kawo tasa a ta adawa.

A yau da Bola Tinubu ya cika aniyarsa ta kayar da gwamnan jiharsa, shekaru 11 bayan ya bar gidan gwamnati, inda shi kuwa Kwankwaso, ya kasa kada nasa gwamnan duk da a 2015 kawai ya bar gidan gwamnati, ya nuna kwankwaso ya sha kasa a nan, kuma akwai abin da zai iya koya daga Bola Tinubu.

Ga sauran bayanai kan yadda Tinubu yayi wa Kwankwaso fintinkau a siyasa:

1. Kwankwaso sai dai ya canja jam'iyya don neman takara, shi kuwa Ja-gaba sai dai a biyo shi a hada jam'iyya a kewayensa.

2. Kwankwaso ya iya munafurcin siyasa da yaudara, kamar yadda yayi a 2011 ga Jonathan, shi kuwa Tinubu yayi alkawari ya cika wa Jonathan a wancan lokaci, bayan da su Buhari suka kasa cika masa muradunsa.

DUBA WANNAN: An sake kwaso gawarwaki daga kududdufin DU

3. Tinubu ya iya biyayya a siyasa, shi yasa yake iya girmama Buhari, ya san gaba-da-gabanta, Kwankwaso kuwa ya kasa biyayya, shi dole sai dai a bishi.

4. Kwankwaso yayi siyasar jagaliya, mai cike da 'yan daba, ga kuma sanya w mabiya uniform na jar hula, manya irinsu Tinubu kuwa sai dai su fada daga jirgi, kuma dole a bisu.

5. Tinubu ya ja da gwamnatin Tarayya ta Obasanjo, ya kai labari a 1999 zuwa 2007, shi kuwa Kwankwaso, ya ja da gwamnatin tarayya ko a 2014 amma ba riba.

6. Tinubu ya iya hakurin damo, ya dafa dutse ko don gobe ya sha romonsa, shi kuwa Gogan naku, kullum ta baka-baka yake yi da zaari, kamar ya rikice.

7. Tinubu yafi karfin yayi takarar sanata, sai dai ya aiko yaransa, shi kuwa kwankwaso har yanzu iyakarsa Senate,

8. Kwankwaso bazai iya dora kowa gwamna ba a yankin arewa, Tinubu shi yake dora gwamnoni a jihohin yankinsa.

9. Kwankwaso zai iya biyu babu daga zaben badi, ya koma hoto, shi kuwa Tinubu, watakil ma a sauke Osinbajo a bashi kujeras in an zarce.

10. Kwankwaso zai iya koyar yadda zai janyo 'yan kudu a jikinsa, ba tare da ya nuna shi ya iya kabilanci da bangaranci ba, Tinubu baya taba batun kabilanci ko bangaranci a fili, sai dai kawai a ga lissafi a kasa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel