Ya zuwa yanzu, abubuwan da aka ciro daga kududdufin mutuwa a kauyen DU

Ya zuwa yanzu, abubuwan da aka ciro daga kududdufin mutuwa a kauyen DU

- An kashe mutane bila adadin an wulla kududdufai na yankin

- Ba'a san ko su waye ba, amma an fi zargin daga kabilun yankin suke

- A baya ansha jin labarin batar fasinjoji da suka bi yankin

Ya zuwa yanzu, abubuwan da aka ciro daga kududdufin mutuwa a kauyen DU
Ya zuwa yanzu, abubuwan da aka ciro daga kududdufin mutuwa a kauyen DU
Asali: Facebook

Al'ummar Najeriya, na cikin kaduwa da yadda ake ta tono gawarwaki da kwarababbun motoci daga karkashin ruwan kududdufi a yankin Du, dake kudancin Jos a jihar Pulato.

An dai zargi kabilun yankin da ko dai sun san me ke faruwa ga masu motoci dake bata a yankin, ko kuma ma sune ke aika-aikar da kansu, ganin yadda har zuwa suka yi don kokarin hana soji aikin tonon ramukan, wadanda sun kai biyar.

Guda daya kawai, ya zuwa yanzu, an tono motoci 18, babura shida, gawarwaki 19, wasunsu sun jibge da rubewa daga kududduin, duk da dai bamu rabbatar da sahihancin wannan bayanai ba.

A karin bayanan da hukumar soji ta saki dai, tace iyaka mota biyu kawai ta samo ya zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: Karin bayani kan kisan gilla a Jos

Anbin takaici kuma, sai abin ya koma zagin kabilanci tsakanin al'ummun kasar nan, musulmi da kirista, inda aka ma karkashe juna a garin Jos, maimakon a bari gwamnati tayi bincike. Wasu ma wai har kira suke aje a kashe kowa a kauyen, wanda ke cike da mata da yawa da manoma, wadanda watakil basune ma ke wannan aika aika ba.

A wani bangaren ma, wasu na gani watakil hadari ne motocin suka yi cikin dare, suka fada kududdufin, ba lallai ko kashe mutane ake ba.

Sai dai, har yanzu ba'a gama bincike ba, ba kuma a san ko gawarwakin akwai ta janar Alkali da ake nema ba.

Su kuma jama'ar yankin, ko tsoro ko hadin baki, sun kasa fitowa suyi bayanin me ke faruwa a wannan gefe nasu mai ban tsoro.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel