Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

Dan Sule Lamido ya lashe takarar kujerar Sanata a PDP

- Dan tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, Mustapha Sule Lamido da wasu mutane biyu sun lashe tikitin takarar Sanata a PDP ta jihar Jigawa

- Mustapha Lamido ya lashe zaben kujerar Sanatan yankin Jigawa ta Arewa ne da kuri'u 4,088 a yankin Jigawa ta Arewa

- Sauran wadanda suka lashe zaben sun hada da Sanata Ubali Shittu da tsohon kwamishinan kudi na jihar, Nasiru Umar Roni

Dan gidan Sule Lamido da ake zargi da arzurta kansa da kudin gwamnati a zamanin babansa a Jigawa, yaci zaben cikin gida na sanata
Dan gidan Sule Lamido da ake zargi da arzurta kansa da kudin gwamnati a zamanin babansa a Jigawa, yaci zaben cikin gida na sanata
Asali: Twitter

Dan tsohon tsohon gwamnan jihar Jigawa, Mustapha Sule Lamido ya lashe tikitin takarar kujerar Sanata na yankin Jigawa ta Arewa a karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A yayin da yake sanar da sakamakon zaben cikin gidan, jami'in zaben yankin Jigawa ta Arewa, Nasiru Barau, ya ce Lamido ne ya lashe zaben fidda gwanin da kuri'u 4,088.

Kazalika, Sanata mai ci a na yankin Jigawa ta Arewa maso Yamma, Ubali Shitu shima ya lashe za zaben fidda gwanin inda ya kayar da wasu 'yan takara uku a jihar.

DUBA WANNAN: Amsar da Buhari ya bawa wata kasa da ta nemi taimakon Najeriya wajen warware matsalolin ta

Idan ba'a manta ba, Shitu yana daya daga cikin Sanatocin da ke goyon bayan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki wanda hakan yasa suka sauya sheka zuwa PDP tare da shi.

A yayin da ya ke sanar da sakamakon zaben, jami'in zaben yankin, Umar Hamza ya ce Mr Shittu ne ya lashe zaben da kuri'u 821 cikin kuri'u 829 da ake tantance na wakilan jam'iyyar masu kada kuri'un.

Har ila yau, wani jami'in zaben, Abdulaziz Usman ya sanar da cewar, tsohon kwamishinan kudi, Nasiru Umar Roni ya lashe zaben Jigawa ta Arewa maso Yamma da kuri'u 1,121 yayin da abokin hammayarsa Jamilu Muhammad ya samu kuri'a daya tak.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel