Kisan miji: Manyan lauyoyi 3 sun janye daga shari’ar Maryam Sanda

Kisan miji: Manyan lauyoyi 3 sun janye daga shari’ar Maryam Sanda

Shari’ar Maryam Sanda, matar da ake zargi da kashe mijinta Bilyamin Bello ya sake daukar sabon salo yayinda manyan lauyoyi uku a tawagar masu kare ta suka janye daga wakilcinsu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Maryam wacce yan sanda suka zarga da haddasa kisan mijinta Bello, dan tsohon shugaban jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Bello Halliru Muhammad na tsare tare da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu, kaninta, Aliyu Sanda da kuma wata Sadiya, wadanda ake zargi da taimaka mata wajen boye duk wani hujja ta hanyar goge jinin marigayin daga wajen da aka aikata laifin.

Kisan miji: Manyan lauyoyi 3 sun janye daga shari’ar Maryam Sanda
Kisan miji: Manyan lauyoyi 3 sun janye daga shari’ar Maryam Sanda
Asali: UGC

An tattaro cewa Joseph B. Daudu (SAN); Rotimi Ogunesan (SAN); A. T. Kehinde (SAN) sun eke ta wakiltan Maryam, Aliyu da Maimuna a shari’an kafin wannan mataki da sukadauka a yanzu, yayinda Olusegun O. Jolaawo daga sashin Messrs Ricky Tarfa & co ke wakiltan Sadiya.

Lauyoyin sun aikawaa kotu wasikar janyewarsu daga shari’an nata.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya koka kan yadda ake kashe rayukan bayin Allah a Jos

Koda dai babu wasu dalilai da aka bayyana a wasikar janyewar nasu, akwai rade-radin cewa ba’a biyansu kudinsu yadda ya kamata. Sai dai ba’a samu tuntubar yan uwan wanda ake shari’a akan ta ba domin tabbatar da lamarin.

Saboda haka ana ganin da wuya zauna sauraron shari’an a ranar Alhamis kamar yadda aka shirya saboda sabon lamarin da billo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.

Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel