Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Mun samu rahoton cewa gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, ya zamto zakaran da ya cafke tikitin takara a zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi na karkashin jam'iyyar APC.

Ko shakka ba bu gwamnan shi ya zamto zakaran gwajin dafi yayin zaben fidda gwani da aka gudanar cikin jihar a ranar Litinin din da ta gabata, inda zai fito kwansa da kwarkwata a babban zabe na 2019.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito, an bayyana sakamakon zaben a Yammacin yau na talata inda gwamna Abubakar ya samu kuri'u 75, 086 yayin da ya lallasa abokin takararsa tsohon ministan 'yan sanda, Dakta Ibrahim Lame, wanda ya samu kuri'u 3,988 kacal.

Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi

Gwamna Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Bauchi
Source: Depositphotos

Sai dai tun a daren jiya wasu 'yan takara uku suka fidda da rai da kuma rashin kyautata zato a yayin da zaben ke ci gaba da gudana.

KARANTA KUMA: Atiku ya bayyana dalilin da ya sanya masu madafan iko ke masa adawa

A yayin bayyana sakamakon zaben a babban ofishin jam'iyyar dake jihar Bauchi, Babban Baturen Zaben, Farfesa Ahmed Bakari, ya bayyana cewa gwamna Abubakar ya yi zarra ga sauran manema tikitin takarar kujerar gwamna na jam'iyyar.

Kazalika jaridar NAIJ.com ta ruwaito cewa, shugabancin jam'iyyar APC yayi watsi da zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamna da aka gudanar cikin kananan hukumomi 20 na jihar Legas da aka gudanar a yau Talata.

Na nan tafe: Shafin NAIJ.com Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mu na ci gaba da godiya a yayin kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ku ceto Leah Sharibu yanzu ba tare da bata lokaci ba – Atiku ga gwamnatin tarayya

Ku ceto Leah Sharibu yanzu ba tare da bata lokaci ba – Atiku ga gwamnatin tarayya

Ku ceto Leah Sharibu yanzu ba tare da bata lokaci ba – Atiku ga gwamnatin tarayya
NAIJ.com
Mailfire view pixel