Kato bayan kato: Ganduje ya bayyana adadin miliyoyin kuri’un da Buhari ya samu a Kano

Kato bayan kato: Ganduje ya bayyana adadin miliyoyin kuri’un da Buhari ya samu a Kano

- A jiya ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da zaben tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2019

- Kamar yadda jam’iyya ta bayyana a baya, ta gudanar da zaben shugaban Buhari kai tsaye, ma’ana kato bayan kato

- Tun da fari jam’iyyar APC ta amince cewar gwamnonin jihohin da take mulki ne zasu kasance manyan jami’an zaben cikin gidan na jiya

A jiya ne jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da zaben tabbatar da shugaba Buhari a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Kamar yadda jam’iyya ta bayyana a baya, ta gudanar da zaben shugaban Buhari kai tsaye, ma’ana kato bayan kato.

Duk da kasancewarsa dan takarar daya tilo daya sayi fam din takarar shugaban kasa a APC, jam’iyyar ta ce sai ta gudanar da zabukan tabbatar das hi a fadin jihohin kasar nan domin yin biyayya ga siyasa da kuma nunawa duniya farin jinin da shugaban keda shi har yanzu a tsakanin mambobin jam’iyyar APC.

Kato bayan kato: Ganduje ya bayyana adadin miliyoyin kuri’un da Buhari ya samu a Kano
Ganduje ya yin bayyana adadin miliyoyin kuri’un da Buhari ya samu a Kano
Asali: Twitter

Da yake sanar da sakamakon zaben jiya a Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar shugaba Buhari ya sanu adadin kuri’u 2,931,235 daga ‘yan jam’iyyar APC dake fadin kananan hukumomi 44 a jihar Kano.

Tun da fari jam’iyyar APC ta amince cewar gwamnonin jihohin da take mulki ne zasu kasance manyan jami’an zaben cikin gidan na jiya.

DUBA WANNAN: Zaben fitar da dan takarar PDP: Ko a kai taron Fatakwal ko kwancewa PDP zani a kasuwa - Gwamna Wike

A wurin da yake sanar da sakamakon zaben, Ganduje ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, sanatan Kano ta Arewa, Kabiru Gaya da takwaransa na Kano ta kudu, Barau Jibrin da kuma hadiman gwamnatin jihar Kano da manyan ‘yayan APC a jihar.

Jihar Kano na daga cikin jihohin APC da suka amince zasu gudanar da zaben fitar da ‘yan takara ta hanyar ‘yar tinke ko kuma kato bayan kato.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel