PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa

- Sanata Binta Garba daga jihar Adamawa tayi ikirarin cewa jam'iyyar PDP tayi kokarin bata cin hanci don ta fice daga APC

- Binta Garba da ta ce an bata N300,000,000 amma ta ki amsar kudin inda ta ce musu ba domin kudi ta ke siyas ba

- Binta Garba za ta fafata da wasu 'yan takara maza uku da ke harin kujerar ta a majalisar dattawa

Sanata Binta Garba mai wakiltan Adamawa ta Arewa ta ce jam'iyyar PDP ta bata cin hancin kudi sama da N300,000,000 domin da fice daga jam'iyyar APC ta koma PDP amma ta ki amincewa ta bukatarsu.

Sanata Garba ta yi wannnan furucin ne a wajen yakin neman zaben ta a Yola gabanin gudanar da zaben fidda gwani a jihar, ta ce PDP ta yi mata alkawarin kudin ne domin ta taimaka wajen rage kuri'un gwamna Mohammed Bindow.

PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa
PDP ta bani cin hancin makudan miliyoyi don na bar APC - Sanatar Arewa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kwance wa gwamnan Legas zani a kasuwa, dukkan yan majalisar jihar basu yinsa

Sai dai daga baya gwamna Bindow da jam'iyyar APC sun lashe zaben gwamna a jihar tare da kujerun sanata uku a shekarar 2015.

Garba ta ce rashin amincewa da tayin da jam'iyyar PDP ta yi mata ne ya kiyaye afkuwar rikici a jam'iyyar ta APC reshen jihar Adamawa.

Sanatan ta na neman takara domin sake komawa majalisar ta dattawa sai dai a halin yanzu akwai wasu 'yan takara maza uku da ke neman fafatawa da ita.

'Yan takarar sun hada da Mai bawa tsohon shugaban Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Mamman Tahir, Tsohon shugaban makarantar horas da lauyoyi kuma Ciyaman din Hukumar Lafiya bai daya, Abdullahi Belel, da Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakilatar Michika da Madagali Adamu Kamale.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel