Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya

- Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Bashir Garba Lado ya janyewa Mallam Ibrahim Shekarau takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya

- A baya Bashir Garba Lado baiyi na'am da tsayar da Mallam Ibrahim Shekarau a matsayin dan takarar Sanatan na Kano ta tsakiya ba

- Domin nuna goyon bayansa, Lado ya bayar da gudunmawar motocci 25 domin cigaba da yakin neman zaben Buhari, Ganduje da Shekarau

Siyasar jihar Kano ta dauki sabon salo yayin da tsohon Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Bashir Garba Lado ya janye takararsa tare da marawa tsohon gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Shekarau baya.

Sanarwan janyewar ta fito ne daga bakin mai bawa gwamna shawara kan al'amuran siyasa, Alhaji Mustapha Buhari Bakwana a yau yayin mubayi'a da kananan hukumomin Dawakin Kudu, Warawa, Kumbutso da Tarauni suka kaiwa Mallam Shekarau a gidansa.

Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya
Siyasar Kano: Lado ya janyewa Shekarau takarar Sanatan Kano ta Tsakiya
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Giwa ta kashe wata da ta dauki hoton ta

A kwanakin baya da gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Malam Ibrahim Shekarau a matsayin dan takarar kukjerar Sanatan Kano ta tsakiya, Lado bai yi maraba da zancen ba domin ya cigaba da yakin neman takararsa.

Sai kuma kwatsam, babban direktan yakin neman zabensa kuma mai bawa gwamna shawara a kan al'amuran siyasa, Alhaji Mustapha Hamza Bakwana ya sanar da cewa Lado ya janye takararsa kuma mai marawa Mallam Ibrahim Shekarau baya.

Domin bayyana cikaken goyon bayansa ga Shekarau, Lado ya bayar da gudunmawar motocci kirar Sharon guda 25 domin kamfe na Buhari, Ganduje da Shekarau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel