Zaben Osun: Ku dakatar da zaben raba gardama, na ci zabe tun ranar Asabar – Dan takarar PDP

Zaben Osun: Ku dakatar da zaben raba gardama, na ci zabe tun ranar Asabar – Dan takarar PDP

Sanata Ademola Adeleke, dan takarar jam’iyyara PDP a zaben gwamnan jihar Osun ya bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kada (INEC) da ta dakatar da zaben raba gardama da take gudanarwa yanzu haka.

Da yake Magana da wakilin jaridar TheCable a gidansa a yau, Alhamis, Adeleke ya zargi hukumar zabe da hada baki da jam’iyyar APC domin yi masa magudi a zaben.

Ya bayyana cewar yanzu haka jihar Osun cike take da jami’an tsaro dake yiwa APC.

“Wannan ba zaben gaskiya da adalci bane. Yaki ake yi a jihar Osun, sun kawo jami’an tsaro sun jibge. Sun hana masu goyon baya na zuwa wurin zabe don kar su kada min kuri’a,” in ji Adeleke.

Zaben Osun: Ku dakatar da zaben raba gardama, na ci zabe tun ranar Asabar – Dan takarar PDP
Dan takarar PDP, Adeleke
Asali: Depositphotos

Adeleke ya cigaba da cewa, “mambobin APC ne kadai ake bari su kada kuri’a. INEC da jami’an tsaro sun hada baki domin bawa APC dammar yin abinda take so a zaben na yau. Babu zabe yau Osun, a saboda haka nake kira ga hukumar INEC da ta gaggauta janye wannan wasan kwaikwayo da ta shirya ta kuma bayyana ni a matsayin sabon gwamnan jihar Osun domin tun ranar Asabar na lashe zabe.

DUBA WANNAN: An kama 'yan PDP dake sojan gona a matsayin jami'an INEC (Hotuna)

A wata hirar daban da ya yi da jaridar Premium Times a gidansa, dan takarar jam’iyyar PDP, Ademola Adeleke, ya nemi shugaba Buhari ya shiga batun zaben raba gardanar na yau don gudun kada ya jawowa Najeriya abun kunya a idon duniya.

Ba iya Adeleke keda wannan ra'ayi na cewar an hana masu goyon bayansa kada kuri'a ba, hatta jam'iyyarsa ta PDP tayi korafin cewar da gan-gan hukumar INEC taki sanar da dan takararta a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun tun ranar Asabar.

Jam'iyyar ta PDP tayi kokarin ganin ba a yi zaben raba gardamar na yau bisa shakkar cewar ba za ai mata adalci ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel