Ma’aikata a jahar Kaduna sun yi fatali da batun shiga yajin aikin kungiyar kwadago

Ma’aikata a jahar Kaduna sun yi fatali da batun shiga yajin aikin kungiyar kwadago

Duk da yajin aikin dindindin da kungiyoyin kwadagon Najeriya suka kaddamar a ranar Alhamis 27 ga watan Satumaba, ofisoshin ma’aikatan gwamnatin tarayya, jihohi dana kananan hukumomi sun aiki a wanann rana, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ma’aikata da dama sun tafi wuraren ayyukansu da suka hada da sakaratiyar Obasanjo house, sakatariyar gwamnatin jahar, bankuna, asibitoci kai hatta a babban bankin Najeriya anyi aiki a yau.

KU KARANTA: Da zaman banza gara aikin kishiya: Tsabagen gardama ta kai wasu matasa ga kirga buhun gero

Wata ma’aikaciyar jinya a asibitin koyarwa na Barau Dikko ta bayyana cewa marasa lafiya da dama sun isa asibitin a ranar Alhamis, kuma ma’aikatan asibitin basu samu wata takarda daga NLC dake nuna an fara yajin aiki ba.

“Mun dai ji an bada umarnin shiga yajin aiki a gidan rediyo, amma babu wani umarni da muka samu a hukumance daga kodai kungiyar kwadago, ko kuma kungiyarmu ta ma’aikatan jinya, amma dai muna sauraronsu.” Inji ta.

Hakazalika majiyarmu ta ruwaito an cigaba da gudanar da ayyuka a babbar kotu dake jahar Kaduna, sai dai kungoyin ma’aikatan sun bayyana cewa zasu tattauna batun shiga yajin aikin ko akasin haka nan bada jimawaba.

Bugu da kari an hangi jami’an kungiyar ta kwadago a baban ofishinsu dake kan titin independence suna ta tururuwa don tattauna hanyoyin tabbatar da ganin ma’aikata sun cika wannan umarni nasu na shiga yajin aikin.

A ranar Laraba 26 ga watan Satumba ne shuwagabannin kungiyar kwadago suka yanke hukuncin shiga yajin aikin sai baba taji don ganin sun tilasta ma gwamnatin Najeriya biyan naira dubu hamsin da shida(N56,000) a matsayin karancin albashi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel