Kungiyar ASUP a jihar Bauchi ba zasu bi sahun NLC wajen shiga yajin aikin kwanaki 7 ba

Kungiyar ASUP a jihar Bauchi ba zasu bi sahun NLC wajen shiga yajin aikin kwanaki 7 ba

- Kungiyar ASUP ta kwalejin kimiyya da kere kere ta kwalejin Tatari Ari da ke jihar Bauchi, ta ce ba zata bi sahun NLC wajen shiga yajin aiki ba

- Shugaban kungiyar , Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba, a wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya a Bauchi

- Ya ce sun yanke wannan hukunci ne don ci gaban ilimi da matasa baki daya

Mr Bala Mohammed, shugaban kungiyar malaman kwalejin kimiyya da kere-kere ASUP na kwalejin Tatari Ari da ke jihar Bauchi, ya ce malaman kwalejin ba za su shiga yajin aikin kwanaki 7 da kungiyar kwadago ta kasa nLC ta bayar da umurni ba.

Mohammed ya sanar da hakan a ranar Laraba, a wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya a Bauchi

Ya kara da cewa malaman kwalejin kimiyya da fasahar ASUP ba za su shiga yajin aikin ba saboda "babu wani jawabi ko sanarwa da aka aiko mana a matsayinmu na kungiya dangane da wannan yajin aikin gama gari da NLC ta shiga"

KARANTA WANNAN: Matakin Omisore na marawa APC baya a zaben jihar Osun abun kunya ne - Femi Kayode

Hoto: Mambobin NLC suna zanga zangar lumana
Hoto: Mambobin NLC suna zanga zangar lumana
Asali: Depositphotos

NLC dai ta umurci dukkanin ma'aikata da su shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 7 a fadin kasar wanda ya fara aiki a ranar Alhamis, 26 ga watan Satumba biyo bayan jinkirin da gwamnatin tarayya take yi na tsayar da sabon albashi mafi karanci ga ma'aikata.

Sai dai, shugaban kungiyar ASUP na kwalejin kimiyya da kere-kere ta Tatari Ali da ke jihar Bauchi ya ce "bayan gudanar da dogon nazari da kuma tattaunawa da uwar kungiyarmu ta kasa, un yanke shawarar ba zamu shiga wannan yajin aiki ba, a matsayinmu na halastacciyar kungiyar ma'aikata kuma muna da 'yanci na daukar kowane mataki."

Ya kara da cewa: "ASUP ba zata shiga yajin aiki ba. A yau (jiya) da na ke maku magana, babu wani malami da ya shaida mani cewa yana so aje yajin aiki. Don haka muna kira ga malamai da dalibanmu, da su halarci dakunan koyo da koyarwar su. Mun yanke wannan hukunci ne don ci gaban ilimi da matasanmu baki daya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel