Uwar Jam’iyya ta rushe shugabancin Jam’iyyar APC a Adamawa

Uwar Jam’iyya ta rushe shugabancin Jam’iyyar APC a Adamawa

Mun samu labari cewa tazarcen Gwamnan Adamawa yana lilo a Jam’iyyar APC mai mulki bayan da Uwar Jam’iyyar ta soke shugabancin Jihar. Mataimakin Shugaban APC na kasa ya bayyana wannan.

Uwar Jam’iyya ta rushe shugabancin Jam’iyyar APC a Adamawa
An soke Shugabancin Jam’iyyar APC a Adamawa daf da zabe
Asali: Depositphotos

Mustapha Salihu wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki a Yankin Arewa-maso-Gabas ya tabbatar da cewa Majalisar NWC ta APC ta rushe shugabancin APC a Jihar Adamawa karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Bilal.

APC tace Bilal yayi kokarin haramtawa wasu ‘Ya ‘yan APC zabe wajen fitar da gwani da za ayi. A dalilin haka ne Uwar Jamiyyar ta hana Bilal da sauran Shugabannin APC a Adamawa shiga cikin zaben da za ayi a makon nan.

KU KARANTA: PDP ta tantace Atiku, Tambuwal da Saraki saura Kwankwaso

Kafin nan ma dai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Babachir Lawan yace APC ta dauki wannan mataki ne domin ayi adalci. Lawal yace rushe shugabancin APC na Jihar da aka yi zai sa ayi zaben kwarai a Jihar Adamawa.

Kwanaki Alhaji Ibrahim Bilal wanda shi ne tsohon Shugaban Jam’iyyar APC a Adamawa ya bayyana cewa ‘Dan takarar Gwamna guda kurum Jam’iyyar ta APC ta sani a 2019 kuma shi ne Mai Girma Umar Jibrilla Bindow.

Daga cikin masu neman kujerar Gwamna Umar Bindow akwai tsohon Shugaban EFCC Nuhu Ribadu da kuma surukin Shugaban kasa Buhari. A Ranar Asabar ne APC za ta fitar da gwanin ta na zaben 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel