Naira miliyan 500: Wata mata na neman diyyar diyar ta a wurin Shugaba Buhari

Naira miliyan 500: Wata mata na neman diyyar diyar ta a wurin Shugaba Buhari

- Wata mata na neman diyyar diyar ta a wurin Shugaba Buhari

- Tace sai ya biya ta Naira miliyan 500

- Har yanzu dai diyar ta na a hannun 'yan ta'adda

Mahaifiyar 'yar makarantar nan ta Dapchi da har yanzu take a hannun 'yan ta'addan, Lear Sharibu da suka sace ta a watannin baya, mai suna Rebecca Sharibu ta shigar da kara a kotu tana neman diyyar Naira miliyan 500 akan batan diyar ta ta.

Naira miliyan 500: Wata mata na neman diyyar diyar ta a wurin Shugaba Buhari
Naira miliyan 500: Wata mata na neman diyyar diyar ta a wurin Shugaba Buhari
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Buhari zai yafewa daya daga cikin barayin gwamnati

Kamar yadda muka samu, mahaifiyar dalibar a cikin karar da ta shigar ta bukaci kotu ta tilastawa shugaba Buhari, ministan shari'a kuma Antoni Janar na gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da kuma Insifekta Janar na 'yan sandan Najeriya su biya ta diyyar ta saboda sakacin su.

Legit.ng ta samu cewa Rebecca din dai ta shigar da karar ne a wata kotu dake a garin Legas inda a ciki ta bayyana yadda ta shiga cikin kuncin rayuwa tun bayan sace mata diyar a watan Fabrairu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a farkon shekarar nan ne dai aka sace 'yan matan makarantar kwana ta garin Dapchi amma daga baya aka maido su duka sai ita kadai ce ba'a maido ba.

A wani labarin kuma, Kimanin kwanaki uku kacal a shiga zaben fitar da gwani 'yan takarar gwamnonin jahohi a karkashin inuwar jam'iyya mai mulki a Najeriya ta APC, gwamnan Borno, Kashim Shettima ya zabi wanda yake so ya maye gurbin sa.

Wanda dai gwamnan ya bayyana goyon bayan sa a gare shi shine Farfesa Babagana Umara Zulum dake zaman kwamishinan gyara da kuma sake tsugunnar da wadanda ibtila'in ta'addancin Boko Haram ya shafa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel