Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba – Kungiyar Buhari tayi gargadi

Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba – Kungiyar Buhari tayi gargadi

Kungiyar kamfen din Buhari/Osinbajo sun gargadi Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki cewa yana iya kasancewa a hanyarsa ta zuwa gidan yari idan yaki mutunta doka game da binciken lamarin fashin bankin Offa.

Kungiyar tayi gargadi a wata sanarwa daga kakakin ta Steve Bayode yayinda take martani ga abunda ta kira a matsayin caccakar da shugaban majalisar dattawan ke yiwa Shugaba Muhammadu Buhari, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kungiyar tace abun dariya ne Saraki dake neman takarar shugabancin kasa karkashin PDP ya bude baki yace yan Najeriya na bukatar kwararren shugaban da zai jagorance su, alhalin bai wanke kansa daga lamarin fashin bankin Offa ba har yanzu.

Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba – Kungiyar Buhari tayi gargadi
Saraki na gab da tafiya kurkuku idan bai yi wasa ba – Kungiyar Buhari tayi gargadi
Asali: Depositphotos

Kungiyar tace lallai kwadayi da rashin sanin abunda ya kamata ne ke rura watar neman takarar shugaban kasa da Saraki ke yi, inda ta bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari alkhairi ne ga Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ministan harkokin Niger Delta, Usani Usani a jiya Talata, 25 ga watan Satumba ya tashi don kare Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana cewa shekaru uku da yayi a kan kujerar mulki a matsayin shugaban kasa yafi shekaru 16 da PDP tayi tana mulki nesa ba kusa ba.

KU KARANTA KUMA: Sake zaben Osun: Omisore ya hadu da Oshiomhole, gwamnonin APC, ya amince da yiwa jam’iyya mai mulki aiki

Usani ya fadi hakan ne yayinda yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan mika wani ginin taro da rijiyar tukaa-tuka mai aiki da hasken rana ga al’umman Ishibori na karamar hukumar Ogoja dake Cross River .

Ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da gagarumin gudun mawa wajen inganta rayuwar mutanen Niger Delta ta fannin ababen mora rayuwa da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel