Hukumar 'yan sanda ta kama jami'anta 23 da aka samu da karbar cin hanci

Hukumar 'yan sanda ta kama jami'anta 23 da aka samu da karbar cin hanci

- An kama jami'an 'yan sanda 23 da wasu ma'aikatan saboda aikata wasu laifuka a jihar Kano

- Laifukan da suka aikata sun hada da cin zalin mutane, karbar rashawa, tsare hanya ba bisa ka'ida ba sauransu

- Hukumar 'yan sandan ta fara gudanar da bincike a kansu kafin daukan matakin hukuncin da ya dace da su

Hukumar yan sanda ta jihar Kano ta kama jami'anta 23 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da ke da alaka da rashawa, karbar kudade hannun jama'a, kafa shingen hanya ba bisa ka'ida ba da sauransu.

An kuma kama jami'in hukumar kiyaye hadura na kasa FRSC da kuma 'yan KAROTA 23 duk dai a jihar ta Kano kan wasu laifuka da suka sabawa dokar aikinsu.

Hukumar 'yan sanda ta kama jami'anta 23 da aka samu da karbar cin hanci
Hukumar 'yan sanda ta kama jami'anta 23 da aka samu da karbar cin hanci
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Rigima: Karuwar da wani direba ya dauko ta gudu da motar maigidansa ta N5m

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, Magaji Ma'aji ya tabbatar da kama jami'an a wata hira da ya yi da manema labarai a ranar Litinin a Kano inda ya ce tuni an tsare jami'an da ake zargi da laifukan da suka sabawa doka.

"Ofishin 'Yan sanda ta Kudancin Kano karkashin jagorancin ACP. Naziru Bello Kankarofi ta samu korafe-korafe guda 35 daga al'umma game da ayyukan 'yan sanda kuma tuni an kama jami'ai 66 an kuma fara bincike kansu.

"Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da karbar cin hanci, rashin bin dokar aiki, keta hakkin al'umma, tsare mutane ba bisa ka'ida ba, kafa shingen haya, yin katsalandan cikin harkokin jama'a da sauransu.

"Cikin wadanda aka kama har da jami'in FRSC guda daya da 'yan Karota 28 da VIO guda daya," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel