Zargin cin hanci: ICPC ta maka Masari a kotu

Zargin cin hanci: ICPC ta maka Masari a kotu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan gwamnati (ICPC) ta gurfanar da tsohon shugaban hukumar tallafawa kananu da matsaikatun masana’antu na kasa (SMEDAN), Mista Bature Masari, a gaban kotu bisa zarginsa da karbar nagoron miliyan N119.8m daga hannun ‘yan kwangila da dama.

A cikin takardar tuhuma 27 da hukumar ke yiwa Masari a gaban kotun gwamnatin tarayya dake Abuja, karkashin Jastis Adebola Adeniyi, ICPC ta ce bincikenta ya tabbatar mata cewar Masari ya karbi cin hancin da sunansa da kuma amadadin wasu ‘yan majalisar tarayya.

Lauyan hukumar ICPC, Mista Henry Emore, ya shaidawa kotun cewar Masari ya karbi cin hancin miliyan N50m a ranar 27 ga watan Nuwamba na shekarar 2014 daga hannun wani kamfani, Hamshakin Ventures Ltd, amadadin wasu ‘yan majalisar wakilai 4 daga jihar Benuwe – Herman Hembe, Emmanuel Udende, Benjamin Aboho da Oker Jev. Masari ya karbi kudin ne kafin bawa kamfanin kwangilar wasu aiyuka da majalisa ta sahalewa mambobin 4 ta hannun hukumar SMEDAN.

Zargin cin hanci: ICPC ta maka Masari a kotu
Zargin cin hanci: ICPC ta maka Masari a kotu
Asali: Twitter

Kazalika an zargi Masari da karbar wasu kudaden, daga N800,00 zuwa miliyan N20,000,000, a matsayin cin hanci daga wasu kamfanoni 12 kafin basu kwangila. Ya karbi cin hancin ne ta hanyar amfani da asusunsa dake bankunan Diamond da Guaranty Trust.

Ya aikata duk wannan badakala ne tsakanin watan Afrilu na shekarar 2014 da watan Yuli na shekarar 2015, kamar yadda lauyan ICPC ya bayyana.

DUBA WANNAN: Jami'an tsaro sun kama shugabannin PDP a jihar Osun

Sai dai Masari ya musanta dukkan wannan tuhuma da hukumar ICPC ke yi masa.

Mahmud Magaji, lauyan dake kare Masari, ya roki kotu ta bayar da belin wanda yake karewa a kan sharuda masu sauki.

Jastis Adeniyi ya amince da bayar da belin Masari a kan kudi miliyan N50m tare da garanto mutum 2 da tilas su kasance sun kai matakin darekta a kowacce hukuma ta gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel