Buhari ya amince da biyan naira biliyan 22 hakkokin tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen Najeriya

Buhari ya amince da biyan naira biliyan 22 hakkokin tsofaffin ma’aikatan kamfanin jiragen Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a biya naira biliyan ashirin da biyu (N22,000,000,000) a matsayin hakkokin tsofaffin ma’aikatan kamfanin jirgin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito ministan kudin Najeriya, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta sanar da haka a ranar Litinin 24 ga watan Satumba a yayin ganawa da manoma labaru, inda tace hakan ya samo asali ne tun lokacin da kungiyar ma’aikatan ta mika ma gwamnati bukatar biyansu hakkokinsu daya kai naira biliyan 78.

KU KARANTA:Mace mau dauke da juna biyu, mijinta, da dansu sun mutu sakamakon abinci mai guba

Sai dai kwamitin da shugaban kasa ya kafa na bin diddigin kudaden gwamnati a karkashin wani kwararre mai suna MK Dikwa ta duba wannan bukata ta tsofaffin ma’aikatan, inda ta tabbatar da hakkokinnasu a matsayin naira biliyan 45.

Da wannan ne shugaban kasa ya amince da biyan naira biliyan 22.68 ga tsofaffin ma’aikatan, kamar yadda ministar kudi Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana a yayin ganawar.

“Bayan shafe shekaru goma sha biyar suna jira, a yau shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a biya naira bilyan ashirin da biyu da miliyan dari shida da tamanin, kasha hamsin na sahihin lissafin hakkokin nasu na naira biliyan 45.3 kenan.” Inji ta.

A wani labarin kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin biyan makudan kudade ga jami’o’in Najeriya na gwamnati da suka kai naira biliyan ashirin (N20,000,000,000) don baiwa kungiyar malaman jami’a damar inganta karatun jami’o’in kasarnan.

A gefe guda kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron koli na majalisar dinkin duniya karo na 73 da zai gudana a cikin satinnan kamar yadda kaakakin shugaban kasa Femi Adesina ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel