Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata

Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata

Kassim Afegbua, tsohon hadimin tsohon gwamnan jihar Edo kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole ya sauya sheka da dubban magoya bayansa zuwa jam’iyyar PDP.

Afegbua wanda ya kasance kwamishinan bayanai a Edo, ya samu tarba daga shugaban jam’iyyar, Cif Dan Orbih, a Okpella, kramar hukumar Etsaako ta gabas dake jihar a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto cewa tsohon hadimin Oshiomhole din yce ya dauki wannan matak ne na komawa tsohuwar jam’iyyarsa saboda rashin aikin ababen more rayuwa a garinsa.

Ya bayana cewa koda dai yayi aiki a karkashin gwamnatin APC a jihar na tsawon shekaru 8, bai gamsu ba saboda jihar bata samu cigaba ba ta fannin hanyoyi a garin Okoella.

Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata
Yanzu Yanzu: Tsohon hadimin Oshiomhole ya sauya sheka zuwa PDP da dubban magoya bata
Asali: Depositphotos

Afegba ya kuma yi korafi akan rashin wutar lantarki a garin sannan yayi korafi akan tsadar kayayyaki a fadin kasuwannin jihar.

Yace mambobin APC na sauya sheka zuwa PDP bisa dalilin rashin kyawun hanyoyi da kuma yasar da garuruwansu da gwamnatin jihar tayi.

Ya bayyana cewa PDP na tausayawa wadanda ambaliyar ruwa ya cika dasu a garin sannan suka ga laifin gwamnatin jihar kan yin jinkiri wajen magance matsalar.

KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufai ya kammala shirin daukan sabbin malaman asibiti 3,059 a Kaduna

Kakakin sauran masu sauya shekar, Cif Ekpen Abu, sun sha alwasin yin aiki tare da jam’iyyar don ganin sun lashe zabe mai zuwa a yankin da jihar baki daya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa PDP tayi has ashen cewa Oshiomhole zai binne APC idan har yayi nasarar zama shugan jam’iyyar na kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel