Ni zan lashe zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar PDP – Inji Makarfi

Ni zan lashe zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar PDP – Inji Makarfi

- Ahmed Makarfi yace ya fi duk sauran ‘Yan takaran PDP cancanta

- Tsohon Gwamnan yace idan aka yi zaben adalci APC za ta sha kasa

- Makarfi yace shi ne ya tarairayi PDP ta kai wannan mataki a yanzu

Ni zan lashe zaben fitar-da-gwani a Jam’iyyar PDP – Inji Makarfi
Makarfi yace shi yayi wa Jam’iya hidimar da ta kawo wannan marra
Asali: Facebook

Labari ya zo mana daga Daily Trust inda daya daga cikin masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Ahmed Makarfi ya bayyana cewa shi zai yi nasara wajen samun tikitin Jam’iyyar PDP domin ya fi kowa cancanta.

KU KARANTA: Babban buri na PDP ta lashe kowane zabe a 2019 - Ahmad Makarfi

Tsohon Gwamnan na Jihar Kaduna yayi wannan jawabi ne a Jihar Kebbi lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman inda ya fadawa manyan PDP a Yankin cewa shi ne yake da abin da duk sauran ‘Yan takaran na PDP ba su da shi.

Sanata Ahmed Makarfi yace sauran ‘Yan takaran na PDP sun cancanta amma sai dai shi ne kurum ya iya rike Jam’iyyar adawar a lokacin da abubuwa su ka sukurkuce har ta kai PDP ta kawo inda ta ke a halin yanzu ake sha’awar ta.

Ahmed Makarfi ya bayyana cewa yayi aiki da jama’a da dama a PDP inda yace ya kawo ziyara Jihar Kebbi ne domin ya gana da jama’a ba wai don yayi kamfe ba. Makarfi ya kuma kara da cewa PDP za ta iya doke Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel