Zaben Osun: Gwamna Aregbesola ya fadi ta cikin sa bayan INEC ta fadi sakamako

Zaben Osun: Gwamna Aregbesola ya fadi ta cikin sa bayan INEC ta fadi sakamako

- Gwamna Aregbesola ya fadi ta cikin sa bayan INEC ta fadi sakamako

- Yace yayi zaton kwaf daya za suyi wa PDP

- Amma yace sune za su yi nasara idan aka kara fafatawa

Gwamnan jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma suka gudanar da zaben gwamna a jihar ranar Asabar din da ta gabata ya fadi abun da ke ran sa jim kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC ta bayyana sakamakon zaben.

Zaben Osun: Gwamna Aregbesola ya fadi ta cikin sa bayan INEC ta fadi sakamako
Zaben Osun: Gwamna Aregbesola ya fadi ta cikin sa bayan INEC ta fadi sakamako
Asali: Facebook

KU KARANTA: Dalilin da yasa ake zuwa zagaye na 2 a zaben Najeriya

Gwamnan jihar wanda wa'adin sa zai kare nan da yan watanni, Rauf Aregbesola ya ce shi yayi zaton za suyi wa jam'iyyar adawa a jihar ta PDP kwaf daya ne a zaben ba sai an je zagaye na biyu.

Legit.ng ta samu cewa gwamnan wanda yayi magana ta bakin mai taimaka masa na musamman akan harkokin yada labarai Mista Sola Fasure haka zalika ya ce suna da yakinin cewa idan an sake yin zaben a ranar 27 ga wata, sune za suyi nasara.

Idan dai ba'a manta ba hukumar zabe ta bayyana zaben ne a matsayin wanda bai kammalu ba tare da bayar da dalilin ta.

A wani labarin kuma, Kasa da kwana daya bayan jagoran darikar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fito da surukin sa, Abba Kabir fom din takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2019, ya kuma kara fito da wasu surukan nasa biyu.

Kamar dai yadda muka samu, Sanatan da yanzu haka yake neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP ya fito ne da surukan nasa takarar kujerun majalisar tarayya a jihar ta Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel