‘Dan shekara 26 daga Najeriya ya zama wanda ya fi kowa albashi a Turai

‘Dan shekara 26 daga Najeriya ya zama wanda ya fi kowa albashi a Turai

Mun samu labari cewa wani Matashi ‘Dan Najeriya mai shekaru 26 mai suna Silas Adekunle ya zama wanda ya fi kowa albashi a cikin Injiniyoyin Duniya da ke fagen kera mutum-mutumi.

‘Dan shekara 26 daga Najeriya ya zama wanda ya fi kowa albashi a Turai
Adekunle yayi ficce a cikin manyan Injiniyoyin Duniya
Asali: UGC

Silas Adekunle ya ciri tutan ne bayan ya soma aiki da kamfanin nan na Apple wanda ake ji da shi a Duniya. Kafin yanzu Adekunle shi ne Shugaban kamfanin Reach Robotics da su ka shahara wajen kere-kere a Duniya.

An haifi wannan Matashi Silas Adekuble a Garin Legas kafin ya koma Kasar Birtaniyya tun yana Saurayi. A Ingila ne Adekunle yayi karatun sa na Sakandare da kuma Jami’a har ya gama da matakin da ya fi kowane.

KU KARANTA: Budurwa 'yar Najeriya ta fallasa wani da ya so kwanciya da ita

A 2013 ne Adekunle ne ya kafa Reach Robotics cikin shekaru 4 har ta kai ya kirkiri wani irin sabon manhaja na zamani. Wannan kamfani ne dai ya fito da Adekunle har ta kai Apple Inc. su ka dauko sa aiki kwanan nan.

Manyan Kamfanoni irin su London Venture Partners ne su ka ba Adekunle gudumuwar Dala Miliyan 10 million har ya kuma samu kwangila da Apple. Kamfanin Apple din ya saye ayyukan sa da kudin ya zarce misali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel