Da dumi dumi: INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben jihar Osun

Da dumi dumi: INEC ta dakatar da sanar da sakamakon zaben jihar Osun

- Hukumar INEC ta kammala bayyana sakamakon zaben kananan hukumo 30 na jihar Osun

- Duk da cewar an gudanar da zaben cikin lumana, sai dai an samu kura a wajen siyen kuri'u

- Sai dai INEC ta ce ba zata iya bayyana sakamakon zaben ba har sai ta kammala wasu gyare gyare

Bayan da jama'a suka kammala kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Osun a jiya Asabar, 22 ga watan Augusta, 2018, a yau Lahadi, INEC ta ce ba zata iya bayyana jam'iyya ko dan takarar da ya lashe zaben gwamnan jihar ba.

Sanarwar sakamakon zaben ya fito ne daga bakin jami'in karbar sakamakon zaben jihar na hukumar ta INEC, Farfesa Afolabi Atanda, inda ya bayyana cewa an samu wasu matsaloli na soke zabe a wasu rumfunan zabe, don haka sai ta kammala zata sanar da sakamako.

Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 254345, yayin da jam'iyyar SDP ta samu kuri'u 128049. Yawan kuri'un jam'iyyar ADP ya kai 49744, inda jam'iyyar ADC ta tashi da kuri'u 7681.

Banbancin kuri'un da ke tsakanin PDP da APC ba wani mai yawa bane, PDP na gaban APC da kuri'u 353.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yanzu yanzu: INEC ta kammala bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Osun

Jami'an tsaro sun dakatar da wasu masoyan PDP daga isa shelkwatar INEC
Jami'an tsaro sun dakatar da wasu masoyan PDP daga isa shelkwatar INEC
Asali: Original

Legit.ng ta ruwaito maku cewa PDP ta samu gagarumar nasara a karamar hukumar Obokun, da kuri'u 10,859 akan kuri'u 7,229 da APC ta samu. Amma APC ce ta samu nasara a karamar hukumar Ilesa ta Gabas da kuri'u 9790 yayin da PDP ta samu kuri'u 8244. APC ta kuma sha kayi a karamar hukumar Ilesha ta Yamma a hannun PDP da kuri'u 7251 akan kuri'u 8286 da PDP ta samu.

Sai dai APC ta samu nasara a karamar hukumar Atakumosa da kuri'u 7073 idan aka hada da kuri'u 5218 da PDP ta samu. A bangare daya kuwa PDP ta lallasa APC a karamar hukumar Atakumosa ta Yamma, da kuri'u 5401 akan kuri'u 5019 da APC ta samu.

Kamar dai Aregbesola. shima Chief Bisi Akande ya sha dakyar a karamar hukumarsa ta Ila da tazarar kuri'u 200, yayin da APC ta samu 8401, ita kuma PDP ta samu 8241.

Zuwa karfe 10:50 na safiyar Lahadin hukumar ta kammala bayyana sakamakon kananan hukumomi 30 na jihar, inda karamar hukumar Osogbo ta zo ta karshe a jerin kananan hukumomin da aka sanar da sakamakon zabensu.

Ya zuwa yanzu, Legit.ng ta gudanar da kidayar kuri'un da kowacce jam'iyya ta samu a zaben gwamnan jihar da ya gudana a jiya.

Ga dai yawan adadin kuri'un da kowacce jam'iyya ta samu:

1. PDP

Yawan kuri'u: 254698

2. APC

Yawan kuri'u: 254345

3. SDP

Yawan kuri'u: 128049

4. ADP

Yawan kuri'u: 49744

5. ADC

Yawan kuri'u: 7681

Duk da cewar an gudanar da zaben cikin lumana, sai dai an samu kura a wajen siyen kuri'u, inda jami'an tsaro suka samu nasarar cafke akalla mutane hudu da laifin baiwa jama'a kudi don su zabi yan takararsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel