Ni ne dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC - Makarfi

Ni ne dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC - Makarfi

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu cewa, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Ahmed Makarfi, ya bayyana cewa ya kasance dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC cikin dukkanin 'yan takara na jam'iyyar PDP.

Tsohon shugaban jam'iyyar ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa tare da amsa tambayoyin manema labarai inda ya ce, a hakikanin gaskiya ba bu wani dan takara da jam'iyyar APC ke matukar shakka tamkar sa a halin yanzu.

Sanata Makarfi ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai kan cewa ana yada jita-jitar zai sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa wata jam'iyya ta daban.

Tsohon Gwamnan na jihar Kaduna ya kada baki da cewa, yana kyautata zaton ummul aba isin wannan jita-jita na yaduwa ne da sanadin jam'iyyar APC, domin kuwa shi kadai dan takara da take shakkun yin gaba da gaba tare da zube ban kwarya wajen fafata takara ta neman kujerar shugaban kasa a yayin zaben 2019.

Ni ne dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC - Makarfi
Ni ne dan takara mafi shakka ga jam'iyyar APC - Makarfi
Asali: Twitter

Kazalika Makarfi ya ci gaba da cewa, akwai yiwuwar wannan jita-jita ta kunno kai ne daga jam'iyyar su ta PDP, a sakamakon yadda wasu mambobin jam'iyyar ke alakanta shi da mutum mai rauni da ba ya da wata cancanta ta tsayawa takarar kujerar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Ribadu ya shiga cikin sahun manema takarar Kujerar Gwamnan jihar Adamawa

Tsohon shugaban jam'iyyar yayin mayar da martani dangane da wannan lamari ya hikaito muhimmiyar rawa ta gani da tsohon shugaban kasa Yar'Adu'a da kuma Shehu Shagari suka taka a kasar nan duk da yanayi na sanyi da rashin kuzarin jiki da ake misalta su da shi.

Ya kara da cewa, yanayi ta fuskar rashin kuzari ba ya daga cikin ababe na tantance ingancin jagora, illa iyaka abinda ke cikin kwakwalwarsa na tsare-tsare da manufofi na jagoranci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel