Zaben Osun 2018: Yan ta'adda sun kai farmaki a rumfar zabe a karamar hukumar Orolu

Zaben Osun 2018: Yan ta'adda sun kai farmaki a rumfar zabe a karamar hukumar Orolu

- Wasu da ake kyautata zaton cewa yan ta'adda ne sun kai farmaki a wata rumfar zabe dake karamar hukumar Orolu

- Kwamishinan zabe na jihar Osun, Mr. Olusegun Agbaje ya tabbatar da faruwar kai wannan hari a zantawarsa da manema labarai

- Ya bayyana ce an gaggauta sanar da jami'in rundunar yan sanda da ke a yankin don daukar mataki

Wasu da ake kyautata zaton cewa yan ta'adda ne sun kai farmaki a wata rumfar zabe dake karamar hukumar Orolu a lokacin da ake ci gaba da kad'a kuri'ar zaben gwamnan jihar Osun, a yau Asabar, 22 ga watan Satumba, 2018.

Wakilinmu ya tattara mana rahoto kan yadda yan ta'addan suka kai farmaki a rumfar zaben, wanda ya tilasta masu jama'a guduwa don tsira da lafiya da rayukansu.

Zuwa yanzu ba a tantance ko akwai wanda aka kashe ko aka jiwa rauni ba, sai dai yan ta'adda sun rinka harbe harbe ta ko ina, tare da gargadar mutane akan su bar wajen rumfar zaben.

KARANTA WANNAN: Karin bayani: Sakamakon zaben gwamnan jihar Osun

An fara kirga kuri'un da aka kada a zaben gwamnan jihar Osun

An fara kirga kuri'un da aka kada a zaben gwamnan jihar Osun
Source: Original

Kwamishinan zabe na jihar Osun, Mr. Olusegun Agbaje ya tabbatar da faruwar kai wannan hari a zantawarsa da manema labarai.

Ya bayyana ce an gaggauta sanar da jami'in rundunar yan sanda da ke a yankin don daukar mataki.

Agbaje ya ce: "An gudanar da zabe cikin lumana kusan ko ina a jihar, illa dai karamar hukumar Orulo inda wasu yan ta'adda suka kai farmaki, amma an sanar da DPO na yankin, ya kuma bamu tabbacin kai daukin gaggawa a wajen da abun ya shafa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Magudin Jarabawa: Gwamnati ta maka dan takarar gwamnan PDP a kotu

Magudin Jarabawa: Gwamnati ta maka dan takarar gwamnan PDP a kotu

Gwamnati ta maka dan takarar gwamnan PDP a kotu bayan ya fadi zabe
NAIJ.com
Mailfire view pixel