Siyasar Kano: Hafizu ya amince da bukatar Kwankwaso, ya sayi fam din takara

Siyasar Kano: Hafizu ya amince da bukatar Kwankwaso, ya sayi fam din takara

Farfesa Hafizu Abubakar, tsohon mataimakin gwamna Ganduje ya sayi fam din takarar kujeran Sanatan Kano ta tsakiya biyo bayan matsin lamba daga tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Majiyar mu dake da kusanci da Farfesa Hafizu ta sanar da mu cewar yanzu haka Farfesan yana Kaduna wurin tantance 'yan takara. Hafizu ya yanke shawarar tsayawa takarar ne domin biyayya ga Kwankwaso.

Da farko Hafizu bai amince da bukatar Kwankwaso ta ya tsaya takarar Sanata ba, sai dai magoya bayansa basu amince da matakin da ya dauka ba.

"Gwamna Ganduje ya taba yiwa Hafizu alkawarin bashi makudan kudi domin ya cire jar hular sa, alamar biyayya ga tsohon Kwankwaso. Amma Farfesan ya fadawa Ganduje cewar ba zai iya cin amanar Kwankwaso ba domin abokinsa ne da suka shafe fiye da shekaru 40", kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito wani na kusa Hafizu ne ya fada mata.

Siyasar Kano: Hafizu ya amince da bukatar Kwankwaso, ya sayi fam din takara
Kwankwaso da yaran sa na siyasa
Asali: Depositphotos

Majiyar ta kara da cewa, "mun yi matukar mamaki cewar Kwankwaso ba takarar gwamna zai tsayar da Hafizu ba ganin cewar mukaminsa na mataimakin gwamna ya ajiye domin biyayya ga Kwankwaso."

DUBA WANNAN: Sule Lamido ya lissafa ‘yan Najeriya 4 da suka fi Buhari gaskiya da kima

Sai dai wata majiya ta bayyana cewar babban zunubin Farfesa Hafizu a wurin Kwankwaso shine yadda a farko ya hada kai da Ganduje domin bankado irin bashin kudin da Kwankwaso ya tafi ya bari da kuma rushe tsarin sa na bayar da ilimi kyauta da kuma rubuta takardar neman a hade jami'ar kimiyya dake Wudil da ta Maitama Sule.

"A lokacin Kwankwaso ya yi fushi da Hafizu amma yanzu a bayyana take ya yafe masa," kamar yadda majiyar ta fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel