Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu

Abinda ya fi muhimmanci wajen samar da nono mai yawa da inganci ga mace mai shayarwa ita ce irin abincin da macen ke ci, hakan yasa yau muka kawo muku wasu na'ikan abinda na gida Najeriya 6 da suka kara yawa da inganta ruwan nono ga uwa mai shayarwa.

Yana da muhimmanci mace mai shayarwa ta rika shan ruwa mai tsafta da abinci mai ruwa-ruwa kamar Shayi da madara, kunu da sauransu.

Ga dai jerin abincin kamar haka:

1. Kunu

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: UGC

Kunu yana daya daga cikin abincin iyaye da kakanni ka bawa mai jego ta sha da zarar ta fara shayar da jaririn da ta haifa musamman a kasar Hausa. Ana iya sarrafa shi da gero ko masara a bawa mai jegon.

DUBA WANNAN: Jihohin da APC bata da hamayya mai karfi, kamar yadda yake a Aso Rock - Ahmad

2. Madarar Shanu

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: Depositphotos

Madarar shanu da daya daga cikin abincin da ke kara yawa da inganci nono ga mai jego. Baya na nonon sauran ababen da ake fitarwa daga nonon kamar kindirmo da man shanu ko Yoghurt duk suna taimakawa suma.

3. Dankalin Hausa

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: Twitter

Dankalin hausa yana dauke da sinadarin potassium da kuma carbohydrate da ke matukar taimakawa wajen kara inganci ruwan nono da kuma magance kasala. Ana iya dafa dankalin a ci da miya ko a sarrafa ta wata hanyar.

4. Karas

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: Twitter

Idan mai jego na fama da karancin ruwan nono sai ta dage wajen cin karas ko kuma saka shi cikin abinci ko miyar dage-dage. Karas na dauke sa sinadarin vitaman A da wasu sinadaren da ke taimakawa wajen kara yawa da ingancin ruwan nono.

5. Alkama

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: UGC

Alkama wadda a turance ake kira Oatmeal tana da sinadarai masu gina jiki kuma ga saukin sarrafawa. Mai jego tana iya sarrafa Oatmeal da madara, gyada domin kara dandano.

6. Shinkafa ta gida

Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Abinci 6 da ke karawa mata yawan madara a nononsu
Asali: UGC

Yana da kyau mai jego da dena amfani da shinkafar da aka sarrafa ta a kasashen waje wanda muka fi sani da shinkafar gwamnati ta koma amfani da tamu shinkafar ta gida saboda ita ke dauke da sinadirai da ke taimakawa wajen inganta ruwan nono.

Yanzu da mai jego ta san dukkan wadanda abincin masu muhimmanci da ke taimakawa wajen ingantawa da kara ruwan nono sai ta rika amfani da su sannu-sannu kuma ya da kyau a rika tuntubar likitoci ko wasu kwararu a fannin lafiya kafin fara amfani da wasu abubuwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel