Rai 1 ya salwanta yayin da 'Yan Shi'a suka yi arangama da Sojoji a jihar Yobe

Rai 1 ya salwanta yayin da 'Yan Shi'a suka yi arangama da Sojoji a jihar Yobe

A yayin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin hukumomin tsaro da kuma kungiyar 'yan Shi'a ta Najeriya, mun samu cewa wani sabon lamari ya yi matukar muni yayin arangamar kungiyar da kuma rundunar sojin kasa ta Najeriya a jihar Yobe.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito mun samu cewa, rai guda ya salwantar tare da jikkatar wasu Mutane uku yayin wata arangama da ta auku tsakanin rundunar sojin kasa ta Najeriya da kuma kungiyar ta 'Yan Shi'a cikin Garin Potiskum a jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa, arangamar da ta auku a ranar Juma'ar da ta gabata ta kunno kai ne yayin da kungiyar ke yunkurin kawo karshen Muzaharar Ashura da ta gudanar da wasu Salloli da misalin karfe 8. 30 n safiyar yau daura da babban Otel dake garin Potiskum.

Rai 1 ya salwanta yayin da 'Yan Shi'a suka yi arangama da Sojoji a jihar Yobe
Rai 1 ya salwanta yayin da 'Yan Shi'a suka yi arangama da Sojoji a jihar Yobe
Asali: Original

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Amdulmalik Sunmonu, ya bayar da tabbacin aukuwar wannan mummunan lamari yayin ganawarsa da manema labarai inda ya bayyana cewa, rikicin ya salwantar da rayuwar wani Mutum guda da kuma jikkatar wasu Mutane uku.

KARANTA KUMA: 'Karin bayani kan babban Jami'in rundunar Sojin kasa da ya ɓace a garin Jos

Yake cewa, kungiyar rundunar sa kai ta JTF ta yi gaggawar kwantar da tarzomar yayin da wasu mambobin kungiyar ta 'Yan Shi'a suka yi yunkurin raba wani jami'in tsaro da Bindigarsa na aiki.

Sai dai a yayin ganawar wani dan kungiyar ta Shi'a da manema labarai, Ibrahim El Tafseer ya bayyana cewa, ba tare da aune ba rundunar soji ta budewa mambobin su wuta da harasashai na Bindiga bayan sun kammala Muzaharar su ta Ashura.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumomin tsaro sun yi arangama da 'yan kungiyar yayin da suke gudanar da makamancin wannan lamari na muzaharar ranar Ashura da ta yi daidai da ranar 10 ga watan farko na Musulci a jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel