Malabu: Kotun Kasar Italiya ta damke wasu Mutanen Najeriya da laifi

Malabu: Kotun Kasar Italiya ta damke wasu Mutanen Najeriya da laifi

Mun samu labari cewa wani babban Alkali mai shari’a a Kasar Italiya ta Turai ya daure wasu Bayin Allah ‘Yan Najeriya 2 bayan ya same su da laifi a wata shari’a da ake yi kan rijiyoyin mai.

Malabu: Kotun Kasar Italiya ta damke wasu Mutanen Najeriya da laifi
Ana zargin Gwamnatin Najeriya da yin ba daidai ba wajen saida wani rijiyar mai
Asali: Depositphotos

Alkalin da ya zartar da hukunci a Garin Milan da ke Kasar Italiya a makon nan ya aika ‘Yan Najeriya zuwa gidan yari ne bayan ya same su da rashin gaskiya a shari'ar da ake yi tsakanin Kamfanin man Shell da kuma Kamfanin Eni.

Yanzu dai Kotu ta kama Emeka Obi da kuma wani Mutumin kasar Italiya Gianluca Di Nardo da laifi. Kotun ta kuma nemi a karbe makudan Dalolin da ke hannun wadannan Bayin Allah bayan rashin gaskiyar su a cinikin ya bayyana.

KU KARANTA: Ba a ji dadin labarin tsaida yunkurin tada jirgin Nigerian Air ba

Ana zargin cewa an yi amfani da cin hanci wajen sayen wani rijiyar mai mai lamba ta OPL 245 a lokacin mulkin Jonathan. An saida rijiyar man ne kan kudi Dala Biliyan 1.3. Sai dai an biya toshiya na makudan Miliyoyin kafin ayi cinikin.

Daga cikin wadana zargin cin hancin ya taba akwai tsohon Ministan man Najeriya Dan Etete. Abin da dai Najeriya ta samu a cikin Biliyoyin kudin shi ne Dala Miliyan 210 kacal. An dai dade ana wannan gagarumin shari’ar a waje.

Daga cikin wadanda ake tuhuma akwai Etete, Eni boss Claudio Descalzi da wani Mutumin kasar wajen mai suna Paolo Scaroni. Kamfanin man Shell da Eni duk su na ikirarin cewa su na da gaskiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel