Kasuwanci sai China, nan gaba kadan zata fara sayar da sassan jiki domin dashe ga wasu

Kasuwanci sai China, nan gaba kadan zata fara sayar da sassan jiki domin dashe ga wasu

- Kasar Chana zata zamo kasar mafi yawa dashen sashi

- A shirye muke da mu sanar da sauran kasashe basirar mu

- Zamu karfafa cigaban aiyukan dashen sassan jiki

Kasuwanci sai China, nan gaba kadan zata fara sayar da sassan jiki domin dashe ga wasu
Kasuwanci sai China, nan gaba kadan zata fara sayar da sassan jiki domin dashe ga wasu
Asali: Twitter

Kasar Chana zata zamo kasa mafi yawan dashen sassan jiki a 2020, inji Huang Jiefu, Daraktan kwamitin dashe da kyautar sassan jiki na kasar.

Dashen sassan jiki irinsu koda, hanta, huh, zuciya da gabbai dai shine mafita ga masu bukatar irin wadannan bangarori, bayan cutuka kamar kansa, olsa, hadari, dayabetis da sauransu.

Huang ya fadi haka ne bude taro kashi na uku na kyautar sassan jiki a Xi'an a ranar juma'a.

DUBA WANNAN: Yadda jarin kamfunna zasu kai tiriliyan a kasar nan

Huang yace masu bada kyautar sassan jiki masu rijista sun kai 615,000 tare da 19,380 da akayi nasarar tiyata, inda ya kai 54,956 na sassan jiki da akayi dashe a 9 ga watan Satumba.

"An samu cigaba ba kadan a bangaren dashen sassan jiki a kasar," Inji Huang.

"A shirye muke da mu sanar wa sauran kasashen duniya fasahar mu."

"Chana zata karfafa cigaban dashen sassan jiki a shari'ance da al'adance," inji Guo Yanhong, mataimakin Daraktan fannin shugabanci na kamashon kiwon lafiya na kasar.

Kasar China dai ta rungumi takanoloji iri-iri da fasahar zamani, duk da ana mata kallon kasar kama karya, musamman ganin yadda a kwanakin nan take ta rushe wuraren ibada na masallatai da coci, tate da kama masu ibada dubbai daga dukkan addinan, inda ta kira su da masu cutar kwakwalwa, da kokarin dakushe tattalin arziki, da kawo al'adun da basu dace da kasar ta Chana ba.

Kasashe da yawa sunyi tir da irin wannan aika-aika, inda suka kira kasar ta kwaminisanci, da cewa zaluncinta yayi yawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel