Hatsarin tankar mai ya yi sanadiyyar babbakewar gidaje 30 da motoci da dama a Neja

Hatsarin tankar mai ya yi sanadiyyar babbakewar gidaje 30 da motoci da dama a Neja

Akalla gidaje Talatin ne suka babbake kurmus a garin Maje dake cikin karamar hukumar Suleja ta jahar Neja yayin da wata tankar mai ta fashe a lokacin da hadari ya rutse da ita, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba a daida lokacin da birkin motar ya tsinke bayan direban motar ya nemeta ya rasa, daga nan sai yayi kan wasu motoci guda uku dake ajiye don yi masa birki.

KU KARANTA: Kotun Najeriya ta daure wani dan kasuwa tsawon shekaru 140 a Kurkuku saboda laifin daya aikata

Sai dai koda motar ta ci karo da motocin, bata tsaya ba har sai data kutsa kai cikin wasu gidaje da shagunan dake gefen hanya, nan da nan kuma yasa ta kama ci da wuta bal bal.

Sai dai cikin ikon Allah babu mutum ko daya da ya rasu a sakamakon wannan hadari, kamar yadda jami’an hukumar kare haddura ta kasa, FRSC suka tabbatar.

Ga wasu daga cikin hotunan hadarin:

Hatsarin tankar mai ya yi sanadiyyar babbakewar gidaje 30 da motoci da dama a Neja

Hatsarin
Source: Depositphotos

Hatsarin tankar mai ya yi sanadiyyar babbakewar gidaje 30 da motoci da dama a Neja

Hatsarin
Source: Depositphotos

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Bidiyon Ganduje na karbar daloli: Dalilin da ya sa ba zamu iya daukan wani mataki ba - APC

Bidiyon Ganduje na karbar daloli: Dalilin da ya sa ba zamu iya daukan wani mataki ba - APC

Bidiyon Ganduje na karbar daloli: Dalilin da ya sa ba zamu iya daukan wani mataki ba - APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel