Yaki da Ta'addanci: Yadda sojin Najeriya ke fama da mayaqan ISIL a Sahara da kewaye

Yaki da Ta'addanci: Yadda sojin Najeriya ke fama da mayaqan ISIL a Sahara da kewaye

- Bayanai sun nuna cewa kungiyoyin mayaka na ta'adda na kokarin shigowa Najeriya

- Alqaida ita ta baiwa Boko Haram agajin Makamai da Yuro 200,000 a 2009

- ISIL na neman matsuguni a yankin Sahara

Yaki da Ta'addanci: Yadda sojin Najeriya ke fama da mayaqan ISIL a Sahara da kewaye
Yaki da Ta'addanci: Yadda sojin Najeriya ke fama da mayaqan ISIL a Sahara da kewaye
Asali: Twitter

Tun bayan da suka balle daga Boko Haram, ISWA, ko Islamic State in West Africa, wadanda ke karkashin jagorancin dan Muhammad Yusuf, mai biyayya ga IS dake Syria da Iraq, ke fadada ikonsu a yankunan areewa maso gabashin kasar nan.

Sun hada kai da Alqaida ne a baya, wadda ke ayyukanta a Mali da Mauritaniya da ma Algeriya, wadda ke kiran kanta Alqaida a arewacin Afirka tun a 2009 byan sojin Najeriya sun murkushe su.

A wannan marra ne, bayan Boko Haram suka yi mubayi'a ga IS din, don tsoron sabon mulkin Janar Buhari, sai dai su kuma su AlBAghdadi sai suka sauke Shekau kan cewa ya fiye zafi.

A yanzu dai bayan sun balle, bangaren AlBarnawy, wadanda suke kiran kansu ISWA, sun karfafa kai hari kan sojin Najeriya, kuma sun yi musu barna sosai a watannin nan.

DUBA WANNAN: An karyata batun ko ana bin 9mobile biliyoyi na bashi

Sai dai an hada kai, tsakanin sojin Najeriya, da na sauran kasashe makwabta, da ma na Amurka, domin kawo karshen balahirar.

Sojin Amurka, sun kuma ajje jiragensu marasa matuka a yankin Agadez, inda suke aikin leken asiri da kai hare-hare kan mayakan, dake buya a dazuka da Sahara.

A bayanan sirri da suka fito dai, an gano cewa bayan murkushe su da gwamnatin Najeriya tayi, sai Alqaida ta basu makamai da koya musu yakin sunkuru, da kuma gudummawar Yuro 200,000 wadda ta basu damar fara kai hare-hare a 2012.

Gwamnatin Tarayya dai tace tana iyakar kokarinta, duk da cewa wasu lokutan mayakan kan kai harin ba-zata, kuma suyi barna mai yawa, su kumma kwashi makamai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel