Wata budurwa yar bindiga ta bindige mutane 3 har lahira, ta kashe kanta

Wata budurwa yar bindiga ta bindige mutane 3 har lahira, ta kashe kanta

Wata budurwa mai shekaru 26 ta kai hari a wani babban dakin ajiyan kayayyaki a jahar Mary Land na kasar Amurka, inda ta bindige mutane uku har lahira, sa’annan ta dirka ma kanta harsashi, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban Yansandan Harford, Jeff Gahler ya bayyana cewa budurwa tana aikin wucin gadi ne da kamfanin rarraba magunan agajin gagagwa dake Aberdeen Mary Land, sai dai yace har yanzu basu tabbatar da manufarta ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya baiwa iyalan wani Ministansa daya rasu kyautar katafaren gida

Haka zalika Dansansanda yace budurwar dake zama a garin Baltimore, ta yi amfani ne da wata karamar bindiga da tayi ma rajista da sunanta, da kuma alburusai da dama, inda ta bude ma ma’aikatan kamfanin da take aiki da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis 20 ga watan Satumba.

Wata budurwa yar bindiga ta bindige mutane 3 har lahira, ta kashe kanta
Yansanda
Asali: Depositphotos

“Har yanzu bamu tabbatar da manufar wannan matar ba, amma bai yi kama da harin ta’addanci ba.” Inji Dansanda Jeff, sai dai Dansandan bai bayyana sunan matar ba ko na wadanda aka kashe, amma yace wadanda suka jikkata suna samun kulawa a asibiti.

Wannan harin ba shine farau ba a kasar Amurka domin kuwa an saba samun hare haren yan bindiga a kasuwanni, makarantu, da shaguna a kasar, sai dai ba’a saba ganin haka ba a jahar Mary Land, kuma ba kasafai aka saba ganin mata na kai ire iren hare haren nan ba.

Bugu da kari an taba samun wani hari a jahar Mary Land inda wani dan bindiga ya bindige mutane biyar ma’aikatan kamfanin jaridar Gazette, sai dai Yansanda sun tabbatar da cewa dan bindigan ya dade yana yi ma ma’aikatan kamfanin barazana saboda wani labari da suka buga akansa.

Haka zalika kimanin watanni biyar da suka gabata ne aka samu wata mata yar asalin kasar Iran dake aikin kare hakkin dabbobi ta bindige mutane uku a babban ofishin Youtube dake jahar California.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel