Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo

Gwamnatin jihar Oyo tayi karin haske kan rufe gonar Obasanjo

- Ciyaman din Hukumar Tara Haraji na jihar Oyo, Bicci Alli ya yi karin bayani kan rufe Obasanjo Farms

- Mr Bicci Alli ya ce an rufe kamfanin ne saboda rashin biyan haraji ba dalilan siyasa kamar yadda wasu ke hasashe ba

- A halin an bude kamfanin bayan ta biya harajin da ya kamata ta biya kamar yadda Bicci Alli ya fadi

Ciyaman din Hukumar tara haraji na jihar Oyo, Mr Bicci Alli ya ce rufe gidan gonar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da hukumar tayi a kwanakin baya bashi da alaka da siyasa kamar yadda wasu ke yada wa.

Shugaban Hukumar Haraji ta jihar Oyo ya yi karin haske kan rufe gonar Obasanjo
Shugaban Hukumar Haraji ta jihar Oyo ya yi karin haske kan rufe gonar Obasanjo
Asali: Instagram

Mr Alli ya yi wannan jawabin ne yau Alhamis, a garin Ibadan yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a kan rufe gidan gonar ta Obasanjo da ke Ibadan.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

"Ayyukan mu basu da alaka da siyasa, muna yiwa gwamnatin jihar aiki ne domin karbar haraji ta hanyoyin da doka ta tsara.

"Mun kwashe makonni biyu muna wani zagayen aiki, amma abin takaici wasu na kokarin danganta aikinmu da siyasa; babu wata alaka tsakanin rufe gonar da siyasa.

"Mun dauki matakin rufe Obasanjo Farms da ke Ibadan ne saboda kamfanin bata biya harajin da ya kamata ta biya ba.

"Ina farin cikin bayyana maka cewa a yanzu sun biya harajinsu kuma an bude kamfanin sun cigaba da ayyukansu," inji Bicci.

Alli ya yi kira ga 'yan Najeriya su dena alakanta hakokin da ayyukan dan kasa da kuma siyasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel