Rundunar Yansandan jahar Katsina ta yi ram da wasu matsafa da suka fille kan Dansanda

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta yi ram da wasu matsafa da suka fille kan Dansanda

Jami’an rundunar Yansandan jahar Katsina sun samu nasarar damke wasu gungun matsafa sun uku da suka fille kan wani jami’in Dansanda a kwanakin baya a garin Jos na jahar Filato, inji rahoton jaridar The Nation.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunan wannan dansanda da matsafan suka kashe shine Umana Ishaya kurtun dansanda mai muka Sajan dake aiki da runduna ta 56 na yansandan kwantar da tarzoma dake garin Jos.

KU KARANTA: Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina

Kwamishinan Yansandan jahar, Mohammed Wakili ne ya sanar da kama matsafan a yayin wani taron manema labaru da ya gabatar a ranar Alhamis 20 ga watan Satumba a babban ofishin Yansandan jahar Katsina.

Kwamishinan Yansanda Wakili ya bayyana sunayen matsafan kamar haka; Abubakar Sani Kwaya dan shekara 35 daga karamar hukumar Mani, Abubakar Mohammed Soni dan shekara 28 sai kuma bokan dake basu sa’a Husaini Musa mai shekaru 80.

“Mun kama Abubakar ne a garin Mashi na jahar Katsina, yayin da muka kama sauran a garin Jos, daga cikin abubuwan da muka samu a tare dasu akwai idanuwan mutum guda biyu, gatarin da suka datse kan Dansandanmu, wukaken kwakule idanuwan mutane da kuma kayan sawa.” Inji Wakili.

Haka zalika kwamishinan ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun amsa laifukansu, tare da bayyana rawar da kowannensu ya taka, sa’annan ya bada tabbacin shigar dasu kara gaban Kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, Yansandan jahar Katsina sun samu nasarar kama wasu yan fashi da makami a dajin Jino dake cikin karamar hukumar Dayi, daga cikin yan bindigan da suka kama akwai Bola Lawa da Lawal Kabir dukkaninsu yan asalin karamar hukumar Matazu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel