Sabon rikici ya kunno kai a PDP kan zargin wani dan takarar shugaban kasa na yi ma APC aiki

Sabon rikici ya kunno kai a PDP kan zargin wani dan takarar shugaban kasa na yi ma APC aiki

- An nuna ma juna yatsa tsakanin Dankwambo, Turaki da Wike kan zargin cin amanar PDP

- Yan takaran kujerar shugaban kasar biyu su ce basu da masani akan ikirin da gwamnan jihar Rivers yayi

- Dankwambo yace kowa na da yanci tsayawa takara

Yan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sun ki amincewa da ikirarin gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike kan cewa da yayi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ce ke daukar nauyin wasu yan takara a jam’iyyar adawar.

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo da tsohon ministan ayyuka na mussaman, Kabiru Tanimu sun karyata lamarin cewa basu da masaniya akan haka cewa APC na dauka nauyin wani.

Sabon rikici ya kunno kai a PDP kan zargin wani dan takarar shugaban kasa na yi ma APC aiki
Sabon rikici ya kunno kai a PDP kan zargin wani dan takarar shugaban kasa na yi ma APC aiki
Asali: Original

Wike a yayinda yake zantawa da manema labarai yayi zargin cewa wasu yan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP nayiwa APC liken asiri.

Sai dai takwaran Wike na jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya yi watsi da ikirarin gwamnan na jihar Rives, indya bayyana cewa kowani dan takara na da damar yin akara.

KUKARATA KUMA: Gwamnatin Rivers ta nemi ministan Buhari ya amayo N112bn na kadarorin da ya siyar

A nashi bangaren Turaki yace basu tabbatar a kuma basu karyata Wike ba amma dais u basu a masaniya kan wannan zargi asa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel